Skip to main content

Posts

Da Dumi Dumi - An Tsige Shugaba Trump

Majalisar wakilan Amurka sun samu yawan kuri'un da za su kai ga tsige shugaba Donald Trump. Wannan ya tabbatar da shi a matsayin shugaban Amurka na farko da ka tsige har sau biyu. Kuma wannan zai hana ma sa sake rike kowane irin mukamin siyasar kasar nan gaba da kuma bada damar gurfanar da shi don fuskantar tuhuma a gaban kotu. Ga jerin shuwagabannin Amurka da aka taba tsigewa:  A shekarar 1868 an tsige shugaban Amurka Andrew Johnson,  Sai kuma shugaba Bill Clinton da aka taba tsigewa a 1998. Bayan sa kuma sai shugaban Amurka mai barin gado Donald J. Trump shi kuma  a 2019. Bayan nan kuma yau 13 ga watan Janairun 2021 an sake tsige tsohon shugaban a karo na biyu.

An Soma Jefa Kuri'ar Tsige Trump

'Yan majalisar wakilan Amurka yanzu haka sun soma jefa kuri'ar tsige shugaba Donald J. Trump. Sun soma kada kuri'ar ne bayan kammala muhawarar da ta bada damar ci gaba da daukar mataki na gaba, wanda shi ne kada kuri'ar amincewa ko akasin haka. An dai baza dubban jami'an tsaron soji a ko'ina ciki da harabar majalisar dokoki ta Capitol Hill don shirin ko ta kwana. Bayan kammala jefa kuri'ar daga baya za a turawa majalisar dattijai don daukan mataki na gaba da zai iya kai ga tsige shi ko sabanin haka. Idan har haka ta tabbata zai zama kenan Trump shi ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka tsige har sau biyu. Wannan sabon matakin na da nasaba da jawaban shugaban a makon jiya, da 'yan majalisar suka ce sun kai ga tunzura magoya bayansa har suka kai wa majalisar hari da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyar, ciki kuwa har da jami'in dan sanda da ke kare masu zanga-zangar daga kutsa kai ginin majalisar.

Matsalar Tsaro Ta Addabi Jahar Sokoto

A daren jiya Talata ne wasu yan bindiga sukayi dirar mikiya a wani kauye mai suna Chacho da ke karamar hukumar mulki ta Wurno da ke jahar Sokoto. Rahotanni na cewa maharan sun kai wa wani Dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu samame ne da niyyar hallaka shi, amma da hakansu ba ta cimma ruwa ba suka yi awon gaba da mahaifinsa hadi da matarsa da kuma harbin kanensa, tare da karbar kudin da suke mallakarsa ne kimanin naira dubu dari shida da sittin. Maharan sun kuma harbe wani dan banga har lahira, mai suna Malam Rabi'u. Wannan lamarin yawitar hare-hare a jahar Sokoto na neman gagarar kundila, domin kwana daya kawai kafin wannan harin wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wani gari da ke karamar hukumar ta Wurno da suka karbi kudi naira miliyan daya daga hannun wani dan kasuwa kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar kama biyar daga cikin su.

DA DUMI-DUMI 'Yan Majalisar Amurka Sun Soma Zama Don Tsige Trump

'Yan majalisar dokokin Amurka sun soma wani zama na musamman yanzu haka, don shirin tsige shugaba Donald Trump, ana sauran kwanaki 9 kacal a rantsar da zababben shugaban kasar Joe Biden. Kakakin majalisar dattawan kasar Nancy Pelosi a wata hira da tashar talabijin ta NBC, ta ce, "Mista Trump zai fuskanci zahiri ta hanyar girbar abinda ya shuka". Ta ce za su nemi mataimakinsa Mike Pence ya aminta tare da sa hannu akan kudurin dokar da zai nuna amincewa da cewa shugaba Trump bai dace ya shugabanci kasar ba, ko kuma idan har hakan ta ci tura, su soma jefa kuri'ar amincewa da tsige shi a tsakiyar makon nan. Idan har hakan ta tabbata wannan ya nuna Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taba tsigewa har sau biyu. Kuma hakan zai bata ma sa suna da makomar siyasa nan gaba. Masana shari'a na ganin bayan tsige shi, zai iya fuskantar tuhuma akan zargin ingiza magoya bayansa su kai hari da zanga-zanga a majalisar dokokin kasar, domin hana amincewa da zaben Joe ...

Kwalejin Ilmi Ta Sokoto Za Ta Koma Jami'ar Ilmi Ta Sokoto - Tambuwal

Gwanan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya lashi takobin ganin kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari ta koma Jami'ar Horas da Malamai da Fannonin Ilmi Ta Jahar Sokoto. Ya fadi hakan yau litinin a lokacin bukin cikar kwalejin shekaru 50 da kafuwa, karo na 22. Ya yi karin hasken cewa ganin yadda ya dauki sha'anin ilmi da muhimmanci da ma yadda ya ke ware masa kaso mafi tsoka a kasafin kudin gwamnatinsa, zai gana da masu ruwa da tsaki a fannin ilmi da ma mai alfarma Sarkin musulmi don neman shawara akan wannan batu. Ya kara da cewa zai kara ginawa kwalejin karin dakunan kwanan dalibai, domin saukake matsalar cin koso. To amma kuma, wasu da TANTABARA ta zanta da su, na kallon batun a matsayin irin alkawurran  da ya ta bayi na samar da karin Sassan nazarin ilmin kimiyya da liktanci a Jami'ar Jahar Sokoto,  tun shekaru uku da suka gabata, amma suka zama durmukyal da suka ce kalamai ne na rufa ido kawai da ya saba da su. To, sai dai aikin gina asibitin koyarwar jami'ar ...

An Rufe Makarantu Da Wuraren Holewa A Najeriya

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ne ya bayar da umurnin a jiya, cewa dukan makarantu da wuraren shakatawa za su kasance a rufe har tsawon makonni biyar. Gwamnatin ta kuma bayar da umurnin ma'aikata daga mataki na 12 zuwa kasa su yi zaman su a gida, in ban da ma su aikin gaggawa, kamar jami'an kiyon lafiya da sauran su. Wannan matakin ya biyo bayan yadda annobar korona ke ci gaba da hayyaka a Najeriya. Haka ma an jiyo ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire na bayar da umurnin sake bude cibiyoyin killace wadanda suka kamu da cutar. Tuni dai wasu jahohin kasar da suka hada da Legas, Kaduna da Imo suka bayar da damar rufe makarantu tare da gindaya dokoki da ka'idojin yaki da cutar, ta hanyar rufe wuraren rawa da takaita zirga-zirga da kayyade lokacin halartar wuraren ibada da ma saka takunkumi.

Sabuwar Kwayar Cutar Korona Ta Soma Yaduwa

A farkon makon nan a ka gano wata nau'in kwayar cutar korona da ta sha bamban da wacce aka sani. Ita dai wannan sabuwar kwayar cuta ta bulla ne a kasar Burtaniya, in da ta yi nasarar mamaye birnin Landan da gasbascin kasar a yankunan Surrey, Essex, Backshire, Backinghamshire Kent da sauran su. Firaminstan kasar Boris Johnson ya ce a halin da ake ciki yanzu, kwayar cutar na bazuwa ne cikin sauri fiye da ta farko; wanda yanzu haka ta ke kashi 70 cikin dari a mizanin yaduwa. Masana kiyon lafiya a duniya sun bayyana cewa, ba Burtaniya kadai wannan sabuwar korona ta bulla ba, har da da Afirka ta kudu da ma sauran sassan duniya kawai dai ba a kai ga farga da hakan ba ne. A cewar su, Burtaniya dai ce ta yi kwakkafin gano ta saboda tsananin bincike da gwajin da ta fi kowace kasa yi kan wannan cuta. Tuni dai kasashen duniya da suka hada da Jamus, Faransa, Italiya, Austireliya, Iceland, Spaniya, Saudiyya da sauran su, suka dakatar da zirga zirgar jiragen sama tsakaninsu da kasar ...

Da Dumi Dumi - Daliban Makarantar Kimiyya Ta Kankara Sun Iso Gida

Yanzu yanzun nan daliban da aka sace a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kankara da ke jahar Katsina suka iso gida. Yaran su kimanin 340 cikin rakiyar jami'an tsaron soji da 'yan sanda, sun iso fuskokinsu cike da annuri, koda yake dukan su sun yi butu-butu da kura alamar wahala. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi waya da gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari in da ya taya shi murnar samun nasarar ceto yaran. An dai sace yaran a ranar jumu'a da dare da ta gabata a wata makarantar kwana da ke karamar hukumar Kankara a jahar ta Katsina. Gwamnatin jahar ba ta yi cikakken bayanin yadda aka karbo yaran ba, ko da ya ke a bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar da rana an ji wani mai garkuwa da yaran na fadin suna tattaunawa da gwamnati don karbar kudin fansa.

Da Dumi Dumi An Ceto Yaran Da Aka Sace A Katsina

Sakataren gwamnatin jahar Katsina Alhaji Mustapha Inuwa ya fitar da sanarwar cewa an samu nasarar ceto daliban nan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga makarantar kwanan ta Kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina. Ya ce an ceto yaran su 340, kuma yanzu haka suna kan hanyarsu ta isowa jahar daga Tsafen jahar Zamfara. Ana sa ran gobe jumu'a za su gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a sada su da iyayensu. Sauran bayani zai zo nan gaba.

Kungiyar Boko Haram Ta Saki Bidiyon Yaran Da Aka Sace A Katsina

Kungiyar Boko Haram ta saki wani faifan bidiyo da ke nuna yaran nan daliban makarantar kimiyya da ke Kankara a jahar Katsina, kwanaki biyar da sace su. A cikin bidiyon an ga wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar na magana cikin Hausa: "Don Allah ina rokon gwamnati da kada ta yi amfani da duk wasu 'yan sa kai, a rufe dukan makarantu. Kuma sojojin da ke tafe don taimakonmu don Allah su koma, ba za su iya yi wa (mayakan) kome ba". In ji yaron. A can bayan yaron an ga wasu yara kanana masu yawan gaske da ake umurta da su zauna, kuma da ba su fi shekara goma goma ba, suna kuka tare da rokon a taimaka a cece su daga hannun mayakan. Faifan bidiyon mai tsawon minti daya ya nuna yaran cikin kura da alamar gajiya a tattare da su, sakamakon tafiya mai nisa a kasa. Ana kuma jin muryar daya daga 'yan bindigar na gargadin gwamnati da kada ta dauki kowane matakin amfani da karfi. Yana mai jaddada cewa yaran na cikin koshin lafiya. A ranar jumu'ar da ta gabata ne maharan suka y...