Shin kun taba jin labarin abubuwan al'ajabi guda 7 da ake kira Seven Wonders of the World a turance? Idan ba ku taba ba to yau zamu fara kawo mu ku bayani game da su, inda zamu soma da Dalar Giza da ke kasar Misira. Ita dai wannan dala da kuke ganin hotonta a kasa, na da matukar ban mamaki; an gina ta ne dubban shekaru da suka gabata, tun a wajajen 2580 - 2560 kafin haihuwar annabi Isa. Tarihi ya nuna wani basaraken Misira mai suna Fir'auna Khufus ne ya gina ta, a matsayin babbar makabartar bizne manyan sarakunan Masar da aka fi sani da Fir'aunoni, da ma manyan tajiran wancan lokaci. Tsawonta ya kai mita 146.7 wato kafa 481 kenan. Haka ma fadin dalar Giza ya kai mita 230.34 ko kuma kafa 455 kenan. An yi amfani da birki ko bulo na manya manyan duwatsu da girmansu zai kai na mota marsandi, wanda miliyoyin bayi suka turo daga wurare masu nisan gaske zuwa inda aka gina dalar. Tarihi ya nuna an dauki tsawon shekaru 20 ana gina wannan dala kuma a halin yanzu tana da shekaru 3,80...