Skip to main content

Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Kashe Masu Zanga-Zanga A Lekki

 Minjstan watsa kabaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya karyata rahoton kafar yada labaran CNN da ke cewa sojoji sun harbi da dama daga masu zanga-zangar Endsars a Lekki ta jahar Legas.

Ministan ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce gwamnatin Najeriya za ta dauki mataki kan batun, da ya hada da rubutawa kafar ta CNN wasika akan ta karyata rahoton ko kuma duk abinda ya biyo baya kada su yi nadamarsa.

A cikin wani bidiyo da kafar ta watsa an nuna sojoji na harbin masu zanga-zangar da harsashe na kwarai; har ma an ga wasun da aka harba kwance cikin jini.

To sai dai tun a watan Oktoban da lamarin ya faru, hukumomin kare hakkin dan Adam da suka hada da Amnesty International suka fitar da rahotannin zargin harbin bindigar da ake alakantawa da jami'an soji.



Comments