Rahotanni da ke fitowa yanzu haka sun bayyana cewa sabbin magungunnan rikagakafin cutar korona na nuna alamaun tasiri cikin gaggawa.
Kamfunnan Pfizer da BioNtech ne sahun gaba wajen samar da maganin, wanda an yi gwajinsa akan kimanin mutum 43,000 a kasashen duniya daban-daban tare da lura da cewa yana kashe cutar da kashi 94.5 kuma ba hi da illa.
Masana kiyon lafiya a duniya dai sun bayar da shawarar ci gaba da amfani da rigakafin, sakamakon amanna da suka yi da shi.
Ana sa ran samar da adadi mai yawa da zai wadaci al'ummar duniya nan da karshen shekara mai kamawa ta 2021, wanda ake muradin samun kimanin biliyan daya da doriya.
Annobar korona da ta bulla tun a farkon 2020 ta kawowa duniya koma baya, wanda galibin kasashe masu karfin tattalin arziki suka gamu da cikas a bangaren tattalin arzikin, wanda ya shafi sassa da dama da suka hada da suhuri da yawo bude ido da ma cinikayya.
Wannan yunkurin samar da rigakafin dai ana daukar sa a matsayin sabon kandagarki ga annibar Covid-19.
Comments