Skip to main content

LABARI DA DUMI DUMI

 Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar tarwatsa 'yan bindigar da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A kwanan nan 'yan bindigar masu garkuwa da mutane sun kashe akalla mutum 15 kan hanyar tare da jikkata da dama.

Rundunar sojan ta bakin jami'in hulda da manema labarai Manjo Janar Enenche ta ce ta samu rahoton asiri ne dangane da 'yan ta'addan.


Comments

Wadanda aka fi karantawa

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani