Skip to main content

An Yiwa Shugaban Najeriya Allurar Rigakafin Cutar Korona

An yi wa shugaban tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo allurar rigakafin cutar Korona (Covid-19) na kamfanin AstraZeneca, kwana daya kacal da soma aikin allurar a duk fadin kasar.

Idan za a tuna, Gwamnatin Tarayya ta sanar a baya cewa lokacin da allurar rigakafin ta iso Nijeriya, Shugaban kasa da jami'an gwamnati da ma dukkan Gwamnonin kasar za su kasance na farko da za a yi wa rigakafin da za nuna a gidan Talabijin na kasa NTA, domin ya zama misali ga sauran 'yan Najeriya da za su biyo baya.

Likitan shugaban kasanr, Dakta Shu’aibu Rafindadi ne ya yiwa shugaban kasar allurar da misalin karfe 11:53 agogon Najeria 10:53 kenan agogon GMT na safiyar yau din nan Asabar, shi ma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bi sahu nan take.

An kuma basu katinan lantarki da ke dauke da bayanan allurar rigakafin su ta hannun Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA), Dakta Faisal Shuaib.

Najeriya ta samu nasarar karbar allurar ta Oxford a ranar Talata inda ta zama kasa ta uku a Yammacin Afirka da ta karbi allurar bayan Gana da Kwadabuwa.
Cutar Korona dai ta yi mummunan ta'adi ga kasashen duniya, in da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa rabo da aga irin hasarar rayuka irin wannan tun Yakin Duniya Na Biyu.

Comments