Skip to main content

Posts

Littafan Da Abduljabbari Ya Nemi Ya Karanto A Wurin Mukabalar Da Ta Gabata

Abduljabbari Ya Kasa Kare Kansa

Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami'ar Bayaro da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace baya ga kame-kame da Abduljabbar ke yi babu wata tambaya daya tak da ya amsa. Ya kara da cewa a maimakon ya bude wagagen littafan nan da ya zo da su don fiddo da hujja sai kawai ya ce babu lokaci. A kan hala ya yanke hukuncin cewa Abduljabbar Nasiru Kabara ya kasa kare kansa. A na sa bangare Abduljabbar ya nemi a dai sake ba shi wani lokaci, watakila idan ya shirya, kuma ga hujja, zai iya tuba. Sai dai Malam Abubakar Madatai, daya daga masu gudanar da muhawarar, ya roki a sake ba Abduljabbar karin lokacin ya ke ta bukata. Su sun shirya amma ya ce shi bai shirya ba don haka a ba shi karin lokacin, kazalika ya nemi gwamnatin jahar Kano da nan gaba idan an amince da bukatar to a bada damar watsawa a gidajen rediyo da talabijin kowa ya ji ya gani.

Abduljabbari Ya Ce Idan An Ba Shi Sarari Zai Tuba

 Abduljabbari ya koka a kan yadda mukabalar ke tafiya, duk da ya kasa amsa muhimman tambayoyin da aka yi masa. Ya ce mintina 10 da aka ba shi don ya amsa tambayoyin da suka shafi cin zarafin Annabi (s.a.w.) ba za su isa ya kwance littafai kusan 500 da ya zo da su ba. An tambai shi ko a wane hadisi aka kira annabi bunsuru ko arne? Ya ce idan an ba shi karin lokaci zai binciko hadisan ya zo da su amma yanzu an kure shi ba cikin shiri yake ba, kuma gaba daya a cewar sa, babu gaskiya a mukabalar. Ya ce yana son ne ya tsamo mutane daga halakar da ke sa suna yin ridda sakamako rudanin hadisan. Kasancewar wannan kasawa ya sa daya daga Malaman da ke zurara masa tambayoyi Malam Abubakar Madatai ya neme shi da ya tuba ya tabbatar da kuskuren da ya yi. Amma Abduljabbar ya ce ta ya zai tuba a wajen wannan muƙabala, a gaban kowa da kowa, ba tare da ba shi karin lokaci don haduwa ta gaba ba, sannan a ba shi karin wasu hujjoji da suka fi nasa.  Da ya ki tuba, malamin ...

IPOB Leader Nmandi Kanu Arrested

Authorities in Nigeria say Nnamdi Kanu, the leader of the separatist group IPOB, has been arrested. The Minister of Justice and Antoni General Abubakar Malami confirmed the arrest of Mr Kanu at a press conference in Abuja on Tuesday. He added that the IPOB chairman was arrested on Sunday and would be arraigned in court on charges of seeking secession from Nigeria. Kanu is facing charges of treason which has led to him being arraigned before a Federal High Court in Abuja for his campaign for the creation of Biafra through IPOB. He is accused of "uniting extremist groups, spreading false information, possessing illegal weapons and importing illicit goods into Nigeria," Malami said. In April 2017 he was granted bail on medical grounds but escaped from the country. Nigerian security forces later declared IPOB a terrorist organization  

Patience Jonathan Na Cikin Tsaka Mai Wuya

  Mai shari’a T.G Ringim na babbar kotun tarayya da ke Legas ya tsayar da ranar 7 ga watan Oktoba, 2021, don sauraren karar da ke neman a kwace dala mikiyan 5.78 da wasu karin dala biiyan N2.4 da ke da nasaba da uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. A ranar 26 ga watan  Afrilun shekarar 2017, mai shari'a Mojisola Olatoregun ta bayar da umarnin a kwace kudaden na wani dan lokaci bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ce suna da alaka da zambar karkatar da kudade. Hasalima, baya ga wani asusun Patience na sirri mai kimanin dala miliyan 5.78, alkalin ya kuma daskarar da wasu asusun da ke da nasaba da ita ciki har da wani asusun da ta ke a bankin Ecobank tare da ragowar wasu naira biliyan 2.4 da aka bude da sunan kamfunnan La Wari Furniture da Bath Limited. Amma kokarin tabbatar da umurnin ya gamu da cikas kasancewar lauyan Patience, Ifedayo Adedipe (SAN) da Cif Mike Ozekhome (SAN), lauya ma kare kamfunnan La Wari Furniture da Bath Limited, sun nuna turjiya k...

Kasar Isra'ila Na Kaiwa 'Yan Jarida Hari

 GAZA: Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya lalata wani dogon gini a birnin Gaza wanda ke dauke da ofisoshin kamfanin dillacin labarai na Associated Press da sauran kafafen yada labarai a yau Asabar, wannan farmakin sojin ya zo ne kwatsam ba tare da yin gargadi ga mazauna ginin ba, matakin da sojoji suka dauka na yin shiru a yayin fafatawarsu da kungiyar Hamas. Harin ta sama ya zo ne kasa da sa'a guda bayan da sojojin suka umarci mutane su fice daga ginin, wanda kuma ya hada da Al-Jazeera, da sauran ofisoshi da gidajen jama'a. Karfin harin ya ruguje daukacin ginin mai hawa 12, qanda ya haddasa turnukewar ƙura.  Babu wani bayani akan dalilin da ya sa aka kai harin.   Wannan sabon farmakin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani harin sama da Isra’ila ta kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke da yawan jama’a a garin na Gaza da ya kashe Falasdinawa akalla 10 'yan asalin dangi daya, wadanda galibinsu kananan yara ne, a wani hari mafi muni da aka kai a rikicin da k...

Israel Targets Journalists

GAZA: An Israeli airstrike destroyed a high-rise building in Gaza City that housed offices of The Associated Press and other media outlets on Saturday, the latest step by the military to silence reporting from the territory amid its battle with the militant group Hamas. The strike came nearly an hour after the military ordered people to evacuate the building, which also housed Al-Jazeera, other offices and residential apartments. The strike brought the entire 12-story building down, collapsing with a gigantic cloud of dust. There was no immediate explanation for why it was attacked. The strike came hours after another Israeli air raid on a densely populated refugee camp in Gaza City killed at least 10 Palestinians from an extended family, mostly children, in the deadliest single strike of the current conflict. Both sides pressed for an advantage as cease-fire efforts gathered strength. The latest outburst of violence began in Jerusalem and has spread across the region, with...