Skip to main content

Patience Jonathan Na Cikin Tsaka Mai Wuya

 

Mai shari’a T.G Ringim na babbar kotun tarayya da ke Legas ya tsayar da ranar 7 ga watan Oktoba, 2021, don sauraren karar da ke neman a kwace dala mikiyan 5.78 da wasu karin dala biiyan N2.4 da ke da nasaba da uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A ranar 26 ga watan  Afrilun shekarar 2017, mai shari'a Mojisola Olatoregun ta bayar da umarnin a kwace kudaden na wani dan lokaci bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ce suna da alaka da zambar karkatar da kudade.

Hasalima, baya ga wani asusun Patience na sirri mai kimanin dala miliyan 5.78, alkalin ya kuma daskarar da wasu asusun da ke da nasaba da ita ciki har da wani asusun da ta ke a bankin Ecobank tare da ragowar wasu naira biliyan 2.4 da aka bude da sunan kamfunnan La Wari Furniture da Bath Limited.

Amma kokarin tabbatar da umurnin ya gamu da cikas kasancewar lauyan Patience, Ifedayo Adedipe (SAN) da Cif Mike Ozekhome (SAN), lauya ma kare kamfunnan La Wari Furniture da Bath Limited, sun nuna turjiya kan amincewa da shi.

Daga baya lauyoyin biyu sun daukaka kara, in da suke neman ta yi watsi da umarnin kwace kayayyakin na wani dan lokaci tare da kwato kudaden amma Kotun Kolin ta goyi bayan umarnin karamar kotun.

Duk da haka, a tsakiyar lokacin da aka kammala sauraren karar kan kudaden da aka ambata, mai shari'a Olatoregun ya yi ritaya daga daga muminsa a shekarar 2019.

Wannan lamarin ya tilasta wa Alkalin Kotun da ya sake tura batun zuwa ga Mai shari’a Chuka Obiozor don ya saurari hukuncin amma bai saurari karar ba kafin a tura shi Benin.

 A ci gaba da shari’ar a ranar Litinin, Lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, ya yi wa Mai Shari’a Ringim bayanin yadda lamarin ya ke, yayin da lauya mai kare Patience ya sanar da alkalin cewa an dage shari’ar don neman karin bayani saboda ta zo ne a karon farko a gabansa.

Lauyan kamfanonin a nasa bangaren ya bukaci kotun da ta dage shari’ar inda ya ke cewa ta dawo sabuwa fil kuma yana da niyyar shigar da takardar neman kalubalantar gaba dayan yadd aka gudanar da shari’ar.

Ya kuma bukaci kotun da ta ba da dogon lokaci don ba shi damar gabatar da takardar neman hakan.

Da yake amsawa, Oyedepo ya ki amincewa da bukatar sannan ya roki kotun da kar ta bayar da irin wannan a bisa hujjar cewa akwai wani tsari da aka shimfida a Sashe na 17 na Dokar Hukumar Yaki da Almubazzaranci da Dukiyar Jama'a da Sauran Laifuka, wadanda EFCC ta bi diddigi ya zuwa matakin da y sahalewa kotu damar kwace kudaden.

A kokacin zaman kotun Mai Shari'a Ringim ya bayyana cewa shari'ar na da matukar muhimmanci, babu wani mataki da zai iya kakubalantar ta 

 Ya ce, “A ra’ayina na tawali’u, akwai hanyar da za a bi  wajen daukan matakin kalubalantar hukunci ba lallai sai an dage shari'ar ba, wanda a wannan matsayi da aka kai kotu ba ta da qani hurumi na dage shari'ara

 “Amma, kuma kotun ba za ta hana bukatar ba, sakamakon haka, an umarci wanda ake kara na biyu da ya gabatar da bukatar, idan akwai, a cikin kwanaki 14 daga yau, kuma mai shigar da karar zai sami mako guda ya amsa.  Za a saurare shi tare da aiwatar da kudirin kwace kudaden, wanda kuma zai iya zama mataji na karshe.”in ji mai shari'a Ringim.

Mai shari'a Ringim ya dage zaman shari’ar har zuwa ranar 7 ga watan Oktoba, 2021.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.