Skip to main content

Posts

Dalar Amurka Na Fuskantar Barazanar Durkushewa

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya soki kasar Amurka akan irin rawar da dala ke takawa a tattalin arzikin duniya tare da yin kakkausar suka ga asusun lamuni na duniya na IMF. Lula ya yi waɗannan kalamai a wata ziyarar aiki da ya kai Chana, jiya Alhamis a birnin Shanghai a wani bikin kaddamar da takwaransa, Dilma Rousseff a matsayin sabuwar shugabar bankin raya kasashen BRICS, da gamayyar kasashenn Brazil da Rasha da Indiya da Chana da kuma Afirka ta Kudu suka samar. "Me ya sa kowace ƙasa za a danganta da dala don kasuwanci? Wanene ya yanke shawarar dala za ta zama kuɗin duniya?"  Ya ƙara da cewa me yasa banki kamar bankin BRICS ba zai iya samun kuɗin da zai gudanar da hulɗar kasuwanci tsakanin Brazil da Chana ba, da ma sauran ƙasashen duniya? Ya ce yana mamakin yadda ƙasashe cike da rauni  su ke bin sawun amfani da dala wajen gudanar da kasuwanci alhali suna iya hakan da kuɗaɗensu. A wata ganawa tsakanin sa da shugaban Chana Xi Jinping, da kuma ya ...

Tinubu Na Gaban Tambuwal A Sokoto

Asiwaju Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya ba Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP a jihar Sokoto rata a jahar.   Duk da cewa akwai kananan hukumomi 23 a jihar, Tinubu ya tattara mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi 10. Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 101,608, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 98,080 yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya zo na uku da kuri’u 314 sannan Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 171. Kananan Hukumomin Da Aka Samu Sakamakonsu TURETA  Waɗanda aka yi ma rajita: 40,746  Waɗanda aka tantance: 16,516  APC 7, 684  LP.  1  NNPP.  9  PDP.  8, 144  KWARE  Waɗanda aka yi ma rajita 74,056  Waɗanda aka tantance 24,776  APC 10,485  LP.  63  NNPP.  11  PDP.  12,242  BODINGA  Waɗanda aka yi ma rajita 86,139  Waɗanda aka tantance 28,054  A 1 ...

Sakamakon Zaɓen Shugaban Ƙasa Kai Tsaye

Za mu ci gaba da kawo muku sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki na ƙasa. Hoto: BBC Hausa

An Kashe Ɗan Takarar Jam'iyyar Labour A Kudu Maso Gabas

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Kudu maso Gabas hatta a cikin makon da za a gudanar da babban zaɓen 2023. Rahotanni daga yankin sun ce wasu da ba gano ba sun kashe Mista Oyibo Chukwu, ɗan takarar ɗan majalisar dattawa mazabar Enugu ta gabas a ranar Asabar, sa’o’i 48 kafin gudanar da zaɓen. An kashe Chukwu ne tare da wasu magoya bayansa biyar a ƙaramar hukumar Awkunanaw ta Enugu a lokacin da yake dawowa daga wani gangamin yaƙin neman zaɓe. An kuma ce masu kisan sun kona shi da magoya bayansa bayan sun tare da shi a cikin motarsa. Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, waɗanda ke ganin barazana ce ga bunƙasar jam’iyyar a jihar. Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya fito ne daga yankin Kudu maso Gabas, wanda tashin hankali ya zama ruwan dare, tun kafin lokacin zaɓe.  Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sha alwa...

Tsakanin Kyanwa Da Ɓeraye...

Mage ta zauna ta yi jugum ta rasa abinda ke yi mata daɗi, ko ina sai karɓar saƙon zagi da suka take yi daga dabbobin dawa da suka kiwata ta da guminsu saboda yaƙi da ɓeraye. An zargi Mage da ba wa ɓeraye damar sace daddawar jamhuriya ba tare da ɗaukar mataki ba. Ga shi kuma wa'adin mulkin Mage ya ƙare dole ta koma gefe ta zama ƴar kallo. Shin ko me Mage zata yi don kawo ƙarshen ɓarnar ɓeraye da suka tara daddawar jamhuriya don gadar kujerar Mage? Mage ta fesa fiya-fiya akan wannan daddawar miya, wanda yanzu haka ƙwari da ɓeraye suka gano Mage ta shirya ganin bayan su don haka suka haɗa kai domin yaƙar ta. A baya kowane ɓera mai riƙe da ragamar mulki ya ci karensa ba babbaka. Ya yi mulkin mallaka da kama karya. Ya saci daddawar miya son ransa, ya yaƙi duk wanda ya ɗaga masa murya, ya halatta kansa rusa akurkin kaji ba bisa ƙa'ida ba, ya mallake shingayen ƙananan dabbobi ba bisa ƙa'ida ba. Duk da babbar majalisar dokokin zartaswa ta hana su ba su yarda ba, amma a ...

DA DUMI DUMI: CBN Ya Ce Kada Bankuna Su Amshi Tsofaffin Kuɗi

'Yan sa'o'i da fitar da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sanarwar cewa bankuna na iya amsar tsofaffin takardun kuɗin naira 500 da naira 1000 daga hannun jama'a, to sai dai Bankin na CBN ya yi amai ya lashe in da ya ce bai amince bankuna su amshi takardun kuɗin naira ga kowa ba sai dai mutum ya kai kuɗinsa da kansa kamar yadda aka tsara da farko.

Buhari Ya Amince A Kashe Tsohuwar Naira 200

A wani jawabi da ya yi a yau Alhamis, shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya ba Babban Bankin Najeriya CBN umurnin sake fito da tsohuwar naira 200 a hannun al'umma domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara. Buhari ya bayyana cewa an samu muhimman nasarori ta dalilin canjin fasalin kuɗi da aka yi. Ya nunar da cewa yana sane da irin halin matsin da 'yan Najeriya suka shiga, akan haka suna iya amfani da tsohuwar naira 200 sai dai su kai tsofaffin kuɗaɗe da suka haɗa da naira 500 da kuma naira 1000 a bankin CBN. Menene ra'ayinku kan wannan batu?

CBN Insists On Deadline Despite Court Order

The Central Bank of Nigeria CBN has insisted that its February 10th deadline for the validity of old naira notes still stands. The CBN governor, Godwin Emefiele, made the disclosure while briefing the diplomatic community at the ministry of foreign affairs in Abuja. The development comes despite the ex-parte order of the Supreme Court which restrained the federal government from implementing the February 10th deadline, pending the hearing of the matter on February 15th. Emefiele said the situation is substantially calming down since the commencement of over-the-counter payments to complement ATM disbursements and the use of super-agents. He added that there is no need to consider any shift from the deadline of February 10th.

Filin Jiragen Sama Na Malam Aminu Kano Zai Ci Naira Biliyan 700

Ministan suhurin jiragen sama Alhaji Hadi Sirika, ya bayyana cewa majalisar zartaswata ƙasa ta amince da ware fiye da naira biliyan ɗari bakwai domin aikin kwangilar gyaran filin sauka da tashin jiragen na sama na duniya na Malam Aminu Kano, wanda ya ce za kammala a cikin shekara ɗaya rak. Majalisar zartaswa ta ƙasa ta kuma amince da ware naira biliyan ɗari da goma sha bakwai domin gudanar da kwangilar gina cibiyar bincike akan man fetur ta Oloibir a yankin Naija Delta. Ministan ƙasa a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya shaidawa ‘yan jaridar fadar shugaban ƙasa hakan, inda ya ce za a kammala aikin kwangilar a cikin shekaru biyu da rabi. Ya ce tun a 1980 gwamnatin Alhaji Shehu Aliyu Shagari ta soma aikin, amma daga bisani aka yi watsi da shi wanda a yanzu zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da za a ci ga da tunawa da shugaba Muhammadu Buhari a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kotu Ta Tabbatar Da Peter Obi Matsayin Ɗan Takarar Jam'iyyar LP

Kotun ɗaukaka ƙara mai mazuninta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar inda take neman a hanawa Peter Obi na jam’iyyar Labour damar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa. Waɗanda ake ƙarar su ne Hukumar Zaɓe mai zaman kanta, INEC da jam’iyyar Labour da kuma ɗan takararta Mista Peter Obi. Da ta ke yanke hukuncin tare da taimakon alƙalai uku, mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta amince da yin watsi da shari’ar a dalilin rashin cikakkun hujjoji. Alaƙalan kotun sun nemi masu saka ƙarar da su biya waɗanda ake ƙara tarar naira dubu ɗari biyu a dalilin ɓata mu su lokaci.