Kungiyar Malaman Jami'a ASUU ta fitar da wata sabuwar sanarwa a yau litinini 09/05/2022 da ta bayyana sake tsunduma wani sabon yajin aikin makonni 12. ASUU ta bayyana rashin gamsuwa da yadda bangaren gwamnatin tarayya ya dauki lamarin ba tare da muhimmanci ba. Sanarwar ta ASUU ta kuma nunar da yadda gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure yarjejeniyar da suka yi a 2020, tare da cewa babu wata alamar gwamnati da gaske ta ke. Kungiyar Malaman Jami'ar dai ta kwashe wata hudu tana yajin aiki kafin sake saka wani sabon wa'adi a yau na tsawon makonni 12 abinda masana harkar ilmi ke cewa ya gurgunta sha'anin ilmi a Najeriya.