Skip to main content

Posts

Kotu Ta Tabbatar Da Isah Sadik Achida Matsayin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jahar Sokoto

Babbar kotun daukaka kara ta kasa mai mazauninta a Abuja ta tabbatar da Alhaji Isah Sadik Achida a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jahar Sokoto. An dai shafe wata daya ana jayayya a kotu tsakanin Alhaji Isah Sadik Achida da bangaren Mainasara Abubakar da ke tare da Alhaji Abdullahi Salame sai kuma bangaren shugaban majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida. Idan ana iya tunawa dai babban mai saka kara na kasa kuma ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami SAN, ya taba wani ikirari na cewa kotu za ta tabbatar da shugabancin ga Mainasara Abubakar da ke bangaren Hon. Abdullahi Salame, wanda wannan hukuncin ya zama tamkar watsa kasa a fuskar ministan shari'ar da ya yi riga malam masallaci gabanin hukuncin kotu.

Sabuwar Dambarwar Shugabancin APC

Kwana biyu kafin ta gudanar da babban zabenta na kasa, jam'iyyar APC ta sake tsunduma wata sabuwar turka-turka game da makomar wanda za a zaba matsayin sabon shugabanta. A wata hira da BBC Hausa, gwamnan jahar Kebbi Abubakar Atiku Bagudo, wanda kuma shi ne shugaban gwamnonin APC na kasa ya ce yanzu haka sun kasa cimma matsaya akan wanda zai zama shugaban jam'iyyar a ranar asabar mai zuwa. Bagudo ya kara da cewa sun gana da shugaba Muhammadu Buhari akan samar da matsaya, amma kuma sun lura cewa da wuya idan ba zabe za a gudanar ba a maimakon samar da maslaha. Da aka tambai shi ba ya ganin samar da maslaha tamkar an tilastawa wani ne bin abinda ba ya so, shugabana kungiyar gwamnonin ya ce zai yuwu a sulhunta amma idan hakan ta gagara za a bi hanyar da za ta kawo mafita. Sai dai bai yi cikakken bayani akan wace hanya ce da za a bi idan har an kasa yin sulhu tsakanin 'yan takara. Ga alama wannan na nuna irin yadda jam'iyyar za ta fuskanci kalubale gabanin ko ba...

An Tilas Ni Tsayawa Takara - In Ji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bukatar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a karo na biyar, in da ya ce ya wajaba ne ya karba kiran jama'a. Atiku ya yi wannan magana ne a birnin tarayya Abuja lokacin da ya ke sanar da muradin nasa, "Abubuwan da suka ja hankalina na da yawa, muhimmai daga cikin su akwai bukatar samar da hadin kai, tsaro da tattalin arziki, ciyar da bangarorin gwamnatin tarayya gaba da sauran su". Atiku Abubakar na bayyana wannan ne daidai lokacin da gwamnan jahar Sokoto kuma tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa Aminu Waziri Tambuwal shi ma ya bayyana anniyarsa ta tsayawa neman shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar ta PDP. Tambuwal ya ce babu wani da ya fi dacewa ya mulki kasar nan a wannan lokaci da ake ciki idan ba shi ba. Ya bayyana kan sa a matsayin matashi kuma wanda ya goge a harkar siyasa masanin dubarun mulki da ya san makomar Najeriya...

Dole Mai Son Tsayawa Takara Ya Sauka - 'Yan Majalisar Najeriya

'Yan majalisar dattawa da na wakilan Najeriya sun hada guiwa in da suka gudanar da zaman majalisar ranar laraba 22.03.2022 a zaure guda, domin kalubalantar wani hukucin da ke barazana ga dokar da suka kaddamar. Mahukuntan sun yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya reshen jahar Abiya, da ta umurci ministan shari'a Abubakar Malami ya goge sashe na 84 (12) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya haramta ma masu rike da mukamin siyasa tsayawa takara ko jefa kuri'a, kuma ya wajabta ma duk wanda ke neman a zabe shi a 2023 da ya sauka wata shida kafin zabe. Wannan ya jawo cece-ku-ce har ta kai shugaban kasa neman su yi ma dokar kwaskwarima, abinda kuma su ka ki amincewa da shi. A makon jiya dai babban mai sa kara na kasa, Abubakar Malami ya fito ya nuna amincewa da hukuncin babbar kotun, in da ya dauki alkawarin goge dokar. To amma kuma masana harkar shari'a sun yi ca kan wannan hukuncin tare da cewa ya sabawa doka. Fitaccen babban lauyan Najeriya Femi Falana, ya...

Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya

Bayan shafe 'yan kwanaki a birnin Landan na Burtaniya in da aka duba lafiyarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya a sauka Abuja yau da dare.

Malami Ya Ce Zai Bi Umurnin Kotu Ya Goge Sashe na 84 (12)

Ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya ce cikin gaggawa zai bi umurnin wata babbar kotun Najeriya da ta bukaci a goge sashe na 84 da ya tilasta duk masu rike mukaman siyasa aje mukamansu kwana 30 kafin zabe. KUNA IYA KARANTA: http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/babbar-kotun-tarayya-ta-bayar-da.html Malami dai ya tabbatar da cewa, zai yi ma dokar gyaran fuska. Tun da farko dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hannu tare da rokon 'yan majalisar dattawan Najeriya da su yi ma ta kwaskwarima wajen cire wannan sashe, amma suka ki amincewa da wannan bukata. Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan kafin gudanar da babban zaben jam'iyyar APC da zai gudana a ranar 26 ga wannan wata na Maris. Kuma a na ganin zai iya kara haifar da baraka cikin jam'iyyar.

Babbar Kotun Tarayya Ta Bayar Da Umurnin Soke Sashe na 84 Da Ya Hana Masu Rike Da Mukaman Siyasa Tsayawa Takara

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Umuahia, Jihar Abia, ta umurci Babban Lauyan Tarayya da ya gaggauta soke sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.  Yayin da yake rattaba hannu a kan kudirin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta soke sashe na 84 (12), wanda ya haramta wa mambobin majalisar zartaswa tsayawa takara ba tare da yin murabus ba. Shugaban ya kara da cewa, “Sashe na 84 (12) ya kunshi hana masu rike da mukaman siyasa damar kada kuri’a ko zabe a babban taro ko na kowace jam’iyya, domin gabatar da ‘yan takara a kowane zabe.  Sai dai Majalisar Dattawa ta ki yin la’akari da bukatar shugaban kasar, inda ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman a yi wa sashen kwaskwarima, inda ‘yan majalisar suka jaddada cewa gyaran sashe na 84 (12) zai saba wa ma’aikatan gwamnati.  

Illolin Amfani Da Rikitacciyar Jimla A Rubutu Ko Rediyo

Papertrue.blog *" A kokarin hada su da 'yan'uwansu da sanadiyyar rikice-rikice suka rabu ." A yadda harshe ya ke da wuyar sha'ani wajen aikewa da sako, wajibi ne a kaucewa kowace irin jimla mai harshen damo ko mai iya haddasa rudani a kwalkwalwar mai karatu ko saurare. A maimakon haka ya fi dacewa a ce, " A kokarin hada su da 'yan'uwansu da tashe-tashen hankula suka raba" Dalili kuwa kalamar rikici ba ta dace da nan ba saboda ko mutum biyu na iya rikici da juna.  Rikici na nufin jayayya ko rashin yarda da abu da zai iya haifar da rashin matsaya daya, wanda kuma zai kai ga fada. Mutane na iya yin gaba da juna akan rikici na siyasa ko gado. Amma ita kalmar tashin hankali a bayyane ta ke ga mai saurare, sakamakon irin yadda kalmar ta zama tamkar ta yi kaka-gida saboda yadda yankunan arewacin Najeriya ke fama da tashe-tashen hankula. Me Ya Kawo Rudani A Nan? A jimla ta farko mai saurare zai dauka rikicin tsakanin 'yan'uwan ya ke, ...

Bambancin Bayar Da Labari A Rediyo Da Kuma Talabijin

Shi mai gabatar da shiri a rediyo kullum ya sani sauraren sa ake yi, ba kamar yadda ake kallo a talabijin ba, kan haka dole ya yi amfani da  descriptive words, wato kalmomi masu hoto ,  domin mai saurare ya ga hoton abin a kwakwalwarsa, har ma ya ji dadi a ransa. Getty images Ya Misalin Haka Ya Ke Ga Mai Saurare? Mai saurare na bukatar ganin zahirin hoton abinda mai bayar da labari ke fada. Kunnuwa ke sauraren labarin amma kwakwalwa za ta ci gaba da sarrafa hoton abinda ake siffatantawa. Misalain haka shi ne a suranta maka gida ta hanyar zayyano dukan abinda ya mallaka, kamar kofofi biyu hannun riga da juna da farin fenti sai tagogin gilashi ma su karau-karau ga kuma furanni da aka kawata harabarsa farare da jajaye da kuma rawaya. Nan ta ke kwakwalwar mai saurare za ta dauki hoton har yadda za ku iya ganin sa. Ga Misalin Haka: "Gaba daya kankara ta mamaye tsaunukan sun yi fari fat tamkar auduga. A duk shekara irin wannan lokcin sanyi, ruwan gulabe ...

Ranar Bacci Ta Duniya Ta Zagayo

Kowace rana ta Allah na da nata amfani: aiki da karatu da ibada. Majalisar Dunkin Duniya ta kebe kowace rana kamar yadda yau ta zama ranar bacci ta duniya. Shin ko kun san bacci na kara lafiyar kwakwalwa da taimaka ma mai karatu, kuma wadanne lokuta kuka fi jin dadin bacci?