Skip to main content

Posts

President Buhari Opens The Nigerian Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto

President Muhammadu Buhari  declared open the Nigerian Army Chief of Army Staff Annual Conference 2022 in Sokoto. The conference tagged: “Building a Professional Nigerian Army for the 21st Century Security Environment” was commenced at the multipurpose Hall of the International Conference Center Kasarawa, in Sokoto State. President Buhari said Nigerian Army has over the years demonstrated its capacity and zeal in defending Nigeria’s territorial integrity and sovereignty against external aggression and giving aid to civil authority in mitigating internal security challenges in the country. He explained that under his administration from 2015 to date, the Nigerian Army has achived a significant success in fighting against insergency particularly in the Nirth East and North West. He maintained that the troops’ giant strides have led to the mass surrendering of terrorists and their family members in droves. Troops have also maintained this feat, through their operational en...

Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci Ɗalibbai Su Maka ASUU Kotu

Kasancewar zaman tattauna tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da gwamnatin tarayya an tashi dutse a hannun riga, hakan ya fusata gwamnatin tarayyar Najeriya, in da aka jiyo Ministan Ilmin ƙasar, Malam Adamu Adamu na shawartar ɗaliban jami'ar da ke zaman jira a gida na su maka ƙungiyar a kotu. Ministan ya ce dukan alhakin ɓatawa ɗaliban lokaci ya rataye a wuyan malaman jami'a, kuma ya zama wajibi su biya ɗaliban diyya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya za ta saka ƙafar wando guda da malaman ta hanyar ƙin biyansu albashin watannin da suka kwashe ba tare da aiki ba. Wasu daga cikin malaman jami'ar sun fara mayar da martani kan wannan matsaya ta gwamnatin tarayya. Dakta Mansur Isah Buhar, na Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Na amice ɗari bisa ɗari cewa adalci ne kada a biya membobin ASUU albashinsu na tsawo wata shida da suka kwashe suna yajin aiki, saboda kuwa ai ba su yi aikin da ya dace a ce sun y...

Hukumar Lura Da Kafafe Watsa Labarai Ta Najeriya Ta Ƙwace Lasisin Gidajen Rediyo Da Talabijin 52

Shugaban hukumar ta NBC Malam Balarabe Shehu Illela ne ya sanar da hakan a yau jumu’a, in da ya bayyana cewa akwai ɗimbin bashin da ya kai naira biliya 2 da rara da ake biyar gidajen talabijin na African Independent Television (AIT) da Silver Bird Television da aka fi sani da (STV) tare da ƙarin wasu 52. Shugaban hukumar ya ce dokar Najeriya mai Lamba CAP N11, Sashe na 10, ta shekarar 2004 ta ba hukumar NBC wannan dama, kuma tun a watan Mayun bana ne suka wallafa sunayen kafafe watsa labaran da suka kasa sabunta lasisinsu tare da umurtar su da yin haka a cikin mako biyu rak, ko su fuskanci wannan mataki na karɓe mu su lasisi. Wannan matakin dai ana ganin shi ne irin sa na farko a tarihin Najeriya da ya shafi gidajen rediyo mallakar jahohi da masu zaman kansu. Kazalika, masana na fassara shi da wani salon gwamnatin tarayya na yaƙar ‘yancin faɗar albarkacin baki. Wasu daga gidajen rediyo da wannan dakatarwar ta shafa sun haɗa da Gidan Rediyon Rima na Sokoto da Rediyon Jahar K...

Salman Rushdie Na Cikin Mawuyacin Hali

Tun  bayan da wani matashi a birnin New York na Amurka, mai suna Hadi Matar ya sokawa marubucin wuƙa ya ke kwance a wani asibiti a birnin. A jiya lahadi aka gurfanar da mista Mata a gaban wata kotu in da ya musanta laifukan yunƙurin kisan kai da ake zargin sa da yi. Alƙalin kotun Jason Schmidt ya bayar da umurnin ci gaba da tsare shi ba tare da bayar da beli ba har zuwa lokacin da za a sake gabatar da shi a gaban kotun. Wani makusancin Salman Rushdie mai suna Andrew Wylie, ya sanar da cewa  Mista Rushdie na cikin halin mutu-kwakwai-rai-kwakwai sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan da aka daɓa ma sa wuƙa a fuska da wuya da kuma cikinsa, abinda ya kai ga taɓa hantarsa. Kusan shekara 10 kenan Salman Rushdie na famar ɓuya, tun daga lokacin da shugaban addinin ƙasar Iran, Ayatullahi Ruhullah, ya bayar da umurnin a kashe shi tare da saka ladar dala miliyan 3 ga duk wanda ya kashe shi. Sannan a shekarar 2012 gwamnatin ta Farisa ta ƙara wasu dala 500,000 bisa ga na f...

'Yan Jarida Na Shan Ɗauri A Rasha

Wata ‘yar jaridar wani gidan talabijin na Rasha, Marina Ovsynnikova, ta fuskanci ɗaurin wata biyu saboda ta bayyana rashin goyon baya akan mamayar da ƙasarta ke ci gaba da yi wa Yukren. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, wata kotu ta sanar da kama Ovsynnikova da laifin cin amanar ƙasa, sakamakon ɗaga kwalin da ta yi a kusa da fadar Kremlin mai ɗauke da kalaman da ke cewa, “Putin mai kisan kai ne, yara nawa suka mutu sakamakon aikinka, ka gaggauta dakatar da wannan yaƙi”. Gwamnatin Rasha ta daɗe tana ɗaure masu adawa da mamayar da ta ke yi ma Yukren, tare da bayyana yaƙin  da sunan “aikin dakarun soji na musamman” kuma shugaba Putin ya sha alwashin tsare duk waɗanda aka samu da laifin watsa labarun ƙarya  tsawon shekara goma a gidan jarum.

Cire Iyorchia Ayu Daga Shugaban Jam’iyyar PDP Kasada Ce – Debo Ologunagba

A wani zaman sulhu da ake ci gaba da yi a Abuja, gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike da tsohon mataimakain jam’iyar PDP na yankin kudu, Chif Olabode George, na cikin sahun gaba wajen ganin jam’iyar ta cire shugabanta na yanzu, Iyochia Ayu daga muƙaminsa muddin a na neman zaman sulhun ya kai ga haifar da ɗa mai ido. A cewar su, hakan ne kawai zai iya samar da daidaito ga yankin kudancin Najeriya kasancewar ba adalci ne ba ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iya su fito a yanki guda ba. To, amma kuma wannan buƙata ta gamu da cikas in da a yayin hirarsa da manema labarai a Abuja, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ba za ta saɓu ba, domin cire shi kasada ce, da za ta iya jefa PDP cikin sabon ruɗani.  Ya ƙara da cewa, “ai a fili take ƙarara, kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanadar duk lokacin da aka cire shugaban jam’iyya a bisa kowane dalili ne kuwa, to mataimakinsa kan maye gurbinsa kuma ya zama sun fito daga shiya ɗaya. Kazalika, kundin tsarin m...

An Sako Ƙarin Fasinjojin Jirgin Ƙasa Bakwai Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu 'yanci. An sako mutanen ne a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan. Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga 'yan ta'addar domin a sako su ba. Ɗaya daga waɗanda suka shiga sasantawar mai suna Tukur Mamu, ya fada  a wata sanarwa a ranar Laraba cewa shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.  Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani