Skip to main content

Posts

Rikicin Jam'iyyar PDP A Kudu Maso Yamma

   Rikicin jam’iyar PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya na cikin kwale-kwale tun bayan da aka zabi gwamnan jahar Oyo Seyi Makinde jam’iyar PDP ke ganin ya na uwa da makarbiya a dukan lamurran da suka shafi jam’iyar, abinda suka ce na neman mayar da hannun agogo baya; kuma lamarin da wasu shuwagabannin jam’iyyar ke ganin shisshigi ne da kuma tare hanyar wasu. A baya bayan nan gwamna Makinde ya dinga kai kawo a rikicin jam’iyar a jahar Ikiti da ya ce neman sulhu ne da shiga tsakani, amma hakan ya kai ga musayar yawu tsakaninsa da gwamnan jahar Peter Fayose na lokacin, wanda ke yiwa gwamnan jahar Oyon kallon mai goyon bayan Sanata Abiodun Olujinmi da ya tsaya takara tare da shi. A halin yanzu an ji gwamnan na jahar Oyo na kurari da nuna goyon baya akan shari'ar da ake yi wa Fayose, in da Makinde ke ganin ya dace Hukumar Yaki da Zarmiyar Dukiyar Al’umma ta EFCC ta ci gaba tuhumar tsohon gwamnan jahar Ikitin. Rahotanni sun ce an jiyo shi ya na cewa...

Shin Kuna Da Labarin Al'ajubban Duniya 7

 Shin kun taba jin labarin abubuwan al'ajabi guda 7 da ake kira Seven Wonders of the World a turance? Idan ba ku taba ba to yau zamu fara kawo mu ku bayani game da su, inda zamu soma da Dalar Giza da ke kasar Misira. Ita dai wannan dala da kuke ganin hotonta a kasa, na da matukar ban mamaki; an gina ta ne dubban shekaru da suka gabata, tun a wajajen 2580 - 2560 kafin haihuwar annabi Isa. Tarihi ya nuna wani basaraken Misira mai suna Fir'auna Khufus ne ya gina ta, a matsayin babbar makabartar bizne manyan sarakunan Masar da aka fi sani da Fir'aunoni, da ma manyan tajiran wancan lokaci. Tsawonta ya kai mita 146.7 wato kafa 481 kenan. Haka ma fadin dalar Giza ya kai mita 230.34 ko kuma kafa 455 kenan. An yi amfani da birki ko bulo na manya manyan duwatsu da girmansu zai kai na mota marsandi, wanda miliyoyin bayi suka turo daga wurare masu nisan gaske zuwa inda aka gina dalar. Tarihi ya nuna an dauki tsawon shekaru 20 ana gina wannan dala kuma a halin yanzu tana da shekaru 3,80...

Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Da ASUU

 An kai matsaya tsakanin Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU in da gwamnatin tarayya ta amince da bukatunsu. A jiya jumu'a dai ne suka yi wani zama don ganin malaman sun janye yajin aikin da ya dauki watanni bakwai ana yi. A yanzu dai gwamntin Najeriya ta amince da cire malaman daga tsarin albashi na IPPIS wanda suka jima suna turjiya akai, kuma za ta biya malaman albashin duk watannin da su ke bi. Haka ma ministan kwadagon Najeriya Cris Ngige ya tabbatarwa manema labarai cewa, za a karawa malaman jami'ar alwus da zai kai naira biliyan 35 sabanin yadda yake a da na biliyan 30. Ngige ya kuma ce za a ci gaba da tattaunawa kan sabon tsarin albashi na UTAS muddin an kammala tsara shi. A nasu bangare kungiyar malaman jami'o'in sun yi maraba da wannan yunkuri, in da ake ganin matakin ga alama zai iya kawo karshen dogon yajin aikin da aka dade ana yi.

Ba Zamu Bar Korona Ta Haifar Muna Da Bashin Da Zai Ruguza Mu Ba - Antonio Gutarres

 A yau jumu'a sakataren Majalisar Dunkin Duniya, Antonio Gutarres ya bayyana cewa dimbin bashin da annobar korona ta jefa duniya ya wuce misali, baya ga yunwa da tashin hankali da sauran matsaloli da ke addabar kasashe musamman masu tasowa. Yana wadannan kalamai ne daidai lokacin da a karshen makon nan ake shirin gudanar da taron kolin kasashe ashirin masu karfin tattalin arziki na duniya da aka fi sani da G-20.  Ya ce bai kamata bashi ya zama tarnaki ga ci gaban duniya ba. Ana ganin yana wannan magana ne da manufar tursasa manyan kasashe masu arziki da su yi sassauci ga matalautan kasashe a bangaren da ya shafi dimbin bashin da ake bin su. Gutarres ya ce, "kasashe masu arziki kamar Amurka da China ya dace su samar da sassauci da daidaito ga kasashe masu tasowa, domin taimaka mu su farfadowa". Ya yi nuni da irin illar da kin hakan za ta iya haifarwa duniya nan gaba, "kusan hanyar samar da kandagarkin Covid-19 ba ta wuce ta kudi ba, kenan bai dace a ce duk rana ta All...

Saudiyya Ta Harbo Jirgin Saman 'Yan Tawayen Houthi

 Kasar Saudiyya ta yi nasarar harbo wani jirgi maras matuki da aka gano na mayaka 'yan tawayen Houthi ne da ke Yamen. Kasar ta Saudiyya dai ta ce tuni mayakan 'yan tawayen da suka dade suna gwabza fada da gwamnatin Yamen da Saudiyyar ke marawa baya, suka sha alwashin kai ma ta hari. Jirgin maras matuki ya durfafi Saudiyya ne kafin daga bisani gungun kawancen da take dafawa yayi nasarar harbo shi.

Biden Ya Doke Trump A Georgia Da Ratar Kuri'u 12,284

 An kammala kirga kuri'un jahar Georgia da ake takaddama kan ta, in da Joe Biden ya lashe jahar da rata mai yawa. Jahar Atlanta Georgia mai yawan kuri'u miliyan biyar da doriya ta zama sha kallo a idon duniya ganin yadda shugaba Donald Trump ya yi zargin shi ne ya samu nasara a jahar kuma ya nemi sai an sake kirga dukan kurin'un da aka kada. A jiya alhamis da yamma ne aka kammala lissafin da ya kwashe kusan fiye da mako daya a na yi, in da ofishin sakataren gwamnatin jahar ya fitar da wannan sanarwa. Ofishin Brad Raffensperger ya bayyana cewa bayan sake kirga dukan kuri'un da hannu, sakamakon da aka samu tun farko yana nan bai sauya ba. Joe Biden ya doke Donald Trump da yawan kuri'u 12,284, yayin da shugaba Donald Trump ya samu 1,872.