Asiwaju Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya ba Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP a jihar Sokoto rata a jahar. Duk da cewa akwai kananan hukumomi 23 a jihar, Tinubu ya tattara mafi yawan kuri’u a kananan hukumomi 10. Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u 101,608, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri’u 98,080 yayin da Sanata Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ya zo na uku da kuri’u 314 sannan Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 171. Kananan Hukumomin Da Aka Samu Sakamakonsu TURETA Waɗanda aka yi ma rajita: 40,746 Waɗanda aka tantance: 16,516 APC 7, 684 LP. 1 NNPP. 9 PDP. 8, 144 KWARE Waɗanda aka yi ma rajita 74,056 Waɗanda aka tantance 24,776 APC 10,485 LP. 63 NNPP. 11 PDP. 12,242 BODINGA Waɗanda aka yi ma rajita 86,139 Waɗanda aka tantance 28,054 A 1 ...