Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta Najeriya (INEC) ta fitar da sabuwar sanarwa a jiya alhamis 23 ga watan Yuni, 2022 da ke tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin halastaccen dan takarar kujerar dan majalisar dattijai na kasa mai wakiltar kananan hukumomin Machina da Gashuwa da Nguru da Jakusko da Yusufari da Bade da kuma Karasuwa jahar Yobe, in da kuma ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba ta san da wani zaben fidda gwani da aka gudanar ba koma bayan wanda ya wakana a ranar 28 ga watam Mayu. A cewar INEC babu wani dan takara da ta sani face Bashir Sheriff Machina. Tun da farko dai Sanata Ahmad Lawan ne ke wakiltar wadannan kananan hukumomin, wanda hukumar ta bayyana da cewa ya nemi mukamin shugaban kasa a maimakon matsayin da ya ke akai yanzu haka na dan majalisar dattijai. An dai jiyo shugaban jami'iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, a wata hira da sashen Hausa na BBC na bayyana cewa ba su san da wani ba sai sanata Ahmed Lawan, abinda ya jawo cece-ku-ce....