Skip to main content

Posts

An Kama Wasu Daliget Da Kuri'un Bogi

Har yanzu ana ci gaba da jefa kuri'a kuma kimanin jaha 14 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaben fidda gwani na APC da ke gudana a Dandalin Eagles da ke Abuja. Wadannan jahohin su ne Abia da Kano da Katsina da Adamawa da Delta da Cross River da Osun da Ogun da Borno da Neja da Binuwai da sauran su. Zuwa tsakar daren jiya an dan samu tsaiko na awa guda kasancewar an samu wasu daliget da kuri'un bogi, wanda aka dakatar da zaben kafin daga baya a ka ci gaba.

Yahaya Bello Ya Caccaki Buhari

Da ya ke jawabi a lokacin da ake gudanar da shirin zaben fitar da gwani, gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello ya nemi a zabe shi domin ya magance matsalar tsaro da karancin ilmi da ake fama da su yanzu haka a Najeriya. Ya ce, "akwai takaici ace wai yanzu malaman jami'a suna ci gaba da yajin aiki, dalibai na zaune a gida kuma an kasa magance wannan matsala mai saukin magancewa". Yahaya Bello wanda ya ce ba zai jaye ma kowa a neman tikitin shugaban kasa, ya kara da cewa shi matashi ne kuma matasa ya kamata a ba dama su mulki kasar nan ba tsofaffi da suka gaji ba. Ya yabawa shugaba Buhari akan saka hannu a kan dokar ba matasa damar tsayawa takara, in da ya ce abu ne mai kyau. Ya yi kira ga mata da sauran 'yan Najeriya da ya ce ana zalunta da su zabe shi. Dan takarar ya ce "yanzu haka babu tsaro ko kadan kuma an kyale, ana kashe mutane ana kona mu su dukiya kuma ana kallo an zura ido".

'Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Fara Janye Ma Bola Tinubu

Kawo yanzu dai akwai masu neman mukamin shugaban kasa da suka fito kafin fara jefa kuri'a suka bayyana cewa sun janye takararsu kuma sun marawa tsohon gwamnan jahar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Daga cikin su akwai gwamnan jahar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar da Fayemi Kayode da Ajayi Boroffice da tsohon kakakin majilasar wakilai Dimeji Bokole da kuma Gidein Akpabio. Amma Pasto Tunde Bakari ya bayyana cewa shi kam ba zai jaye ma kowa da ga cikin 'yan takara ba, kasancewar "ba su da kyakkyawar manufar gina kasa face rusa ta", in ji shi. Akwai 'yan takara da dama da ya zu haka su ke jiran a fara kada kuri'a da suka hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Ahmed Yariman Bakura da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rotimi Amechi da sauran su. Zamu kawo mu ku karin labari nan gaba.

"Ba Ni Goyon Bayan Kowane Dan Takara" - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bauyana cewa bai zabo kowane dan takara ba, akan haka a bar daliget su zabi wanda 'yan jam'iyya ke so. Bayan ganawa da shugaban kasan jim kadan bayan da shugaban jam'iyyar APC Sanata Abdullahi Adamu ya ayyana Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na APC, karkashin jagorancin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudo, sun ce sun tabbatar ma shugaba Buhari cewa har yanzu suna kan bakansu na mika mulki ga kudu. Wannan dai ya nuna daga gobe takara jam'iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Gwamnonin APC Da Sauran Masu Takara Ba Su Amince Da Zabin Ahmad Lawan Ba

Gwamnonin jam'iyar APC da masu takarar neman mukamin shugaban kasa sun ja daga akan wannan mataki na tsayar da Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sun nemi dole mulki ya koma kudu kuma a gudanar da zaben fidda gwani. Labarin da ke shigowa yanzu haka ya nunar da cewa za a fafata a zaben fidda gwani tsakanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu da Kayode Fayemi da David Umahi da sauran su a Dandalin Eagles da ke Abuja a gobe talata. Za ku ji sauran bayani daga baya.

Stepping Down Not The Right Option - Osinbajo

Vice president Yemi Osinbajo has denied reports that he intends to step down for a certain presidential aspirant ahead of the presidential primary of the All Progressives Congress (APC). The denial is contained in a statement by the chairman of Osinbajo’s campaign council, Richard Akinnola on Sunday. According to the statement, the people behind the speculation are “afraid of the huge political support base of the Vice President, Prof. Yemi Osinbajo,” adding that the VP is ready for the presidential primary scheduled to hold between June 6 and 8. The campaign council “welcomes our distinguished delegates from across the country to Abuja for our presidential primaries. “As you settle down in Abuja, we implore you to kindly disregard various fake news making the rounds that Prof. Yemi Osinbajo has stepped down. “Osinbajo would be hoping to clinch the ticket of the ruling party with much desire to take over from his principal, President Muhammadu Buhari at the end of his tenur...

Gwamnatin Buhari Ta Ce Za Ta Samar Da Hanyar Saukar Da Farashin Abinci

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fara lalubo zaren kawo karshen matsalar hauhawar farashin abinci a Najeriya. Ministar ta ce za a fito da wata hanyar yin taron kasa da masu ruwa da tsaki domin samar da matakin da za a dogara gare shi wajen rage ma 'yan kasa radadi cikin gaggawa. Idan ana iya tunawa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kulle kan iyakokin kasar da zimmar bunkasa noma abinda ya haifar da tsananin tsadar abinci.

PDP Na Son Sake Zaben Fidda Gwani A Jahar Bauchi

Rahotanin da ke shigowa yanzu haka na cewa an samu rabuwar kai tsakanin manyan shugabannin jam'iyyar PDP a jahar Bauchi in da jam’iyar ke shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna a jahar. Wannan ya biyo bayan matakin da  Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya dauka ne, da ya kekasa kasa ya ce ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba. Jaridar Daily Trust da DW Hausa duka sun ruwaito wannan labari.

Abubakar Gada Da Salame Sun Janye Daga Zaben Fidda Gwanin APC A Sokoto

Sanata Abubakar Gada da Abdullahi Balarabe Salame sun fitar da sanarwar janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamna a jahar Sokoto bayan wata takaddama da ta biyo baya. Takardar da suka fitar ta bayyana cewa tun farko sun nemi a yi zaben ta hanyar 'yar tinke, amma kuma wani bangare na jam'iyyar ya yi watsi da wannan. Sun ce ganin ba za a yi mu su adalci ba ya sa ba za su shiga zaben ba, kuma suna kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta duba yuwar bin bukatar da suka nema tun da farko. A cewar takardar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa duk zaben da aka yi ba tare da amfani da masu zaben 'yan takara da aka fi sani da delegate, ko kuma ta hanyar sulhuntawa ba to haramtacce ne. Kan haka suke neman uwar jam'iyyar da ta san dacewa ba a yi zabe a jahar Sokoto ba, kuma wannan zai iya jawo jam'iyyar APC ta rasa dan takara, in ji su.

Zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jahar Sokoto A Jam'iyyar PDP Ya Bar Baya Da Kura

Bayan da gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci zaman sulhu domin tsayar da dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP tare da zabar Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma, hakan ya haifar da cece-kuce tsakanin jama'a. Daga cikin jerin 'yan takarar da suka nemi kujerar akwai mataimakin gwamnan jahar Sokoto, Alhaji Maniru Muhammed Daniya da kwamishin muhalli na jahar Sokoto, Alhaji Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon sakataren gwamnatin jahar Sokoto, Alhaji Sa'idu Umar Ubandoma da kuma tsohon mataimakin gwamnan jahar Sokoto Alhaji Muktari Shagari. Bayan zama da gwaman Aminu Waziri Tambuwal ya yi da dukan su a dakin taro na kasa da kasa da ke Kasarawa, daga karshe gwamnan ya tabbatar da Sa'idu Umar Ubandoma a matsayin wanda zai yi ma jam'iyyar PDP takarar gwamna a 2023. Rahotannin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da cewa shi ma daya daga 'yan takarar da bai yi nasara ba, Alhaji Muntari Shagari ya fice daga jam'iyar ta PDP sai d...