Gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan watsa labaran jahar, Muhammad Garba da na ma'ikatar addin musulunci Muhammad Tahar ne suka sanar da kafar BBC Hausa lokacin da za a gudanar da mukabila da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara. Bangaren gwamnatin ya fitar da ranar lahadi 7 ga watan gobe na Maris a matsayin ranar da malaman jahar Kanon za su gwabza da Malamin. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma yi alkawarin samar da cikakken tsaro a lokacin gudanar da muhawarar ta ilmi. Wannan bukatar da malamin ya dade yana nema sai a wannan karo ya samu amincewar gwamnati a hukumance. TANTABARA za ta kawo muku yadda muhawarar za ta kasance.