Skip to main content

Da Dumi Dumi An Saka Ranar Mukabila Da Malam Abduljabbari Kano

Gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan watsa labaran jahar,  Muhammad Garba  da na ma'ikatar addin musulunci Muhammad Tahar ne suka sanar da kafar BBC Hausa lokacin da za a gudanar da mukabila da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.
Bangaren gwamnatin ya fitar da ranar lahadi 7 ga watan gobe na Maris a matsayin ranar da malaman jahar Kanon za su gwabza da Malamin. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma yi alkawarin samar da cikakken tsaro a lokacin gudanar da muhawarar ta ilmi.
Wannan bukatar da malamin ya dade yana nema sai a wannan karo ya samu amincewar gwamnati a hukumance.
TANTABARA za ta kawo muku yadda muhawarar za ta kasance.

Comments