Skip to main content

Posts

Me Ku Ka Sani Game Da Labari Maras Daɗi (Negative Story)?

Recent posts

Sheƙar Tsuntsu Da Ta fi Kowace Girma A Duniya

A kan samu irin wannan sheƙar tsuntsun a ƙasashe kudancin Afirka irin Botswana da Namibiya. Abin mamaki shi ne wani ɗan ƙaramin tsuntsu ne mai suna Philetairus socius kan yi wannan sheƙa .   Ta yi kama da saƙar zuma, kuma ya kan nemi bishiyoyi masu ƙarfi kamar gawo da bagaruwa da farar ƙaya sannan ya yi wannan sheƙa. Ta kan jure ruwan sama da zafin rana har ma da tsananin sanyin hunturu. A cikin sheƙa ɗaya akan samu ɗakuna kamar ɗari, ƙofofin kusa da juna. Masu nazarin rayuwar tsuntsaye na ganin wannan tsuntsu shi ne irin sa na farko a duniya ɗan ƙarami da kan gina sheƙa mai girma kamar wannan. Faɗin sheƙar ya kan iya kai har ƙafa 20 tsawonta kuma ƙafa 10. 

Barista Yunusa Ari Ya Yi Ɓatan Dabo

Dakataccen kwamishin hukumar zaɓe na jahar Adamawa, Barista Yunusa Hudu Ari, ya ranta cikin na kare jim kaɗan bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a gudanar da cikakken bincike game da badaƙalar da ake zargin sa da ita. Kakakin hukumar INEC Festus Okoye ne ya sanar da gidan talabijin na Channels haka. Okoye ya ce su kansu ba za su iya cewa ina ya shiga ba saboda tun bayan faruwar lamarin ba ya ɗaukar kiran waya kuma sun ma daina jin ɗuriyarsa gaba ɗaya. Da aka tambai shi ko akwai wani mataki da hukumar INEC za ta ɗauka kan wannan sabon lamari, sai ya ce, "ai wannan hakkin jami'an tsaron 'yan sanda ne na tabbatar da sun san inda yake. Idan har jami'an tsaro na buƙatar gurfanar da shi, su ne za su iya zaƙulo shi tare da gabatar da shi a gaban shari'a". Hudu Ari dai ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jahar Adamawa a ranar Lahadin makon jiya, inda ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun gabanin a kammala tat...

INEC Ta Nemi A Kama Kwamishinan Da Ya Sanar Da Sakamakon Zaɓen Adamawa

Bayan kammala wani zaman tattaunawa a jiya talata da Hukumar ta INEC ta yi a Abuja dangane da dambarwar da ta faru a jahar Adamawa.  Hukumar ta fitar da sanarwar matakin da ta ɗauka a shafinta na twitter, inda ta yi kira ga Sifetan 'yan sanda na ƙasa da ya gurfanar tare da tuhumar tsohon kwamishinan zaɓen jahar Barista Hudu Yunusa Ari. Ta kuma nemi Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya ja hankakin hukumomin da ke da alhakin naɗa kwamishinonin zaɓe domin ɗaukar matakin da ya dace. Wannan dambarwar ta soma ne tun daga ranar Lahadi lokacin da kwamishinan zaɓen ya ayyana A'ishatu Ɗahiru Binani a matsayin wadda aka zaɓa gwamnar jahar Adamawa gabanin a kammala tattara sakamakon zabe.

Tsaunin Hin Sam Wan Mai Ɗimbin Shekaru A Duniya

Tsaunukan Hin Sam Wan , da kuma aka fi sani da Dutsen Whale Uku, wasu tsaunuka ne ma su ban sha'awa da suka kai kimanin shekaru miliyan 75.  Suna cikin daga tsaunukan ƙasar Thailand masu ban mamaki.  Sunansu ya samo asali ne daga kamanninsa, idan aka dubi tsaunin daga sama daga sama za a ga ya yi kama da dangin whales wato dabbar nan ta tekun mai kama da kifi whale.

Putin Ya Ziyarci Sansanin Soja Na Kherson Da Ke Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ziyarci yankunan Ukraine da aka mamaye a karo na biyu tun bayan ƙaddamar da wani gagarumin farmaki, kamar yadda fada Kremlin ta sanar a yau Talata. Putin ya ziyarci hedkwatar soji a yankin Kherson na kudancin ƙasar Ukraine da kuma hedkwatar tsaron Rasha da ke yankin Luhansk. Tafiyar ta zo ne a daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare a gabashin Ukraine. Jaridar ƙasar Rasha ta The Moscow Times   https://www.themoscowtimes.com/2023/04/18/putin-visits-occupied-ukraine-territories-a80862 ta bayyana cewa Fadar Kremlin ba ta bayyana takamaiman lokacin da tafiyar ta gudana ba kuma hotunan ziyarar biyu sun nuna Putin sanye da tufafi daban-daban.

Binani Na Neman Kotu Ta Tabbatar Da Ita Wadda Ta Lashe Zaɓen Adamawa

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Adamawa a ranar Litinin sun fito kan tituna domin nuna adawa da ayyana Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa. Sai dai ita Binani ta buƙaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) daga sauya matakin da aka ɗauka na ayyana ta da a ka yi a matsayin wadda ta lashe zaɓen.  A wata buƙata da ta shigar a ranar Litinin, mai neman izinin kotun ya nemi izinin kotun ta ba ta damar shigar da buƙatar neman umarnin haramtawa INEC daga ɗaukar duk wani mataki na watsi da sanarwar da aka yi a ranar 16 ga Afrilu da Kwamishinan zaɓen jahar, Barista Hudu Ari ya ayyana ta a matsayin wadda ta samu ƙuri'u mafifi rinjaye kuma ta lashe zaɓen alhali ba a kammala tattara sakamakon zaɓen gaba ɗaya ba. Ta kuma nemi a ba da umarnin hana hukumar zabe ta INEC, da wakilinta nadawa ko kuma duk wanda ke wakiltarta daukar wasu matakai na bayyana wanda ya lashe zaben gwamna da ak...

Takalman Fir'auna

Takalman Zinariya na Fir'auna Tutankhamun, na daula ta 18 wadda ya yi mulki shekaru 1,300 kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Yanzu haka waɗannan takalman na nan a Gidan Adana kayan Tarihi na Masarautar Alƙahira da ke Misira 📷 Saliadeen Sicey

Ko Kun San Yadda Gidajen Samudawa Su Ke?

Samudawa su ne mutanen Annabi Saleh (AS) waɗanda ke da girman jiki da tsawo tamkar bishiyar dabino.   Waɗannan wasu daga gidajen Samudawa ne da suka rage a halin yanzu. Ana kiran wajen da suna (Mada’in Salih) ko Al-Hijr da Larabci,  (ٱلْحِجْر‎‎). Yankin na nan a Al-‘Ula cikin lardin Madina a Hejaz, ta ƙasar Saudiyya. A shekarar 2008, Hukumar Kula Da Adana Kayan Tarihi Ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ayyana Mada’in Salih  a matsayin wani wajen da take girmamawa, wurin tarihi na Hegra  na nan nisan kilomita 20 arewa da garin Al-‘Ula, tafiyar mil 250 arewa maso yammacin birnin Madina. Samudawa sun wanzu shekaru ɗari bakwai da goma sha biyar kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Mutane daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci wurin, domin ganin ikon Allah.

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Filato

Rahotanni sun ce an kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a yankin Mai Tumbi da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni da aka tura ‘yan sanda domin tabbatar da zaman lafiya a yankin da rikincin ya shafa Babban Daraktan Hukumar Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya a Jihar Filato Joseph Lengmang, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce sun yi matuƙar baƙin ciki da yadda lamarin ya faru, inda rahotanni masu tayar da hankali suka nuna cewa matsalar tsaro ta tabarbare a yankin, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuwa da dukiya mai ɗimbin yawa.