Skip to main content

Posts

Ba Za Kara Sace Kowa Ba A Najeriya - Inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen ci gaba da satar jama'a a fadin Najeriya. An dai jiyo hakan ne a ta bakin Ministan sufurin jiragen sama na kasa, Sanata Hadi Sirika lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin tarayya don yiwa gwamnatin jahar Zamfara jaje, akan daliban Makarantar Kimiyya ta 'Yan Mata ta Jangebe su kimanin 300 da aka sace. Sirika ya ce wannan shi ne na karshe, domin kuwa gwamnatin tarayya za ta dauki sabbin matakai da za su taimaka wajen dakushe ayukkan ta'addanci da suka mamaye yankunan arewa. Ya kara da cewa Buhari ya nuna damuwarsa matuna kan yadda ayukkan ta'addanci ke dada raruwa. Shugaban kasar ya kuma yabawa gwamnan jahar Zamfara saboda kokarinsa wajen yaki da matsalar tsaro. Shi ma gwamnan jahar Zamfara, Bello Mutawalle ya bayyana jin dadi akan yadda gwanatin tarayya ke nuna kulawarta akan wannan lamari.

No More Abduction In Nigeria - Says Buhari

Nigerian President Muhammadu Buhari has assured Nigerians that abduction of 300 female students from Government Girls Science Secondary School, Jangebe, Zamfara State, would be the last to happen in the country. Minister of Aviation, Senator Hadi Sirika, conveyed Buhari’s declaration when he led a high-powered federal government delegation to sympathise with the people and government of Zamfara State. According to him, 'Buhari is assuring the citizens there would be no abduction again because the Federal Government would show its commitment in fighting banditry and other forms of insecurity in the country’.  The minister said new measures have been developed by the federal government which would bring complete end to all forms of criminality in the nation. Sirika said the president is agitated by the setback and increase of banditry in almost everywhere in the north, which he noted that would not be tolerated. Buhari also commends zamfara State Governor, Bello Matawalle...

Gunmen Killed Suswam Elder Brother

Gunmen in a car have killed Terkula Suswam, the elder brother of former Benue State Governor Gabriel Suswam. They also killed his aide in an attack that occurred at Anyiin in Gaambetiev of Logo Local Government Area at about 8.40 pm in the late evening. An eyewitness said he was working outside his compound when a Toyota car, speedily approached him. The source said the victim suspected the vehicle’s occupants to be gunmen and attempt to run into the compound before he was shot. Recent attacks and kidnapping in Nigeria lead thousand of people to leave their homes and instead end up as refugees in other places and this stuation put many in dillema.

NDLEA Arrests A Dangerous Transborder Drug Trafficker

The National Drug Law Enforcement Agency has arrested a transborder drugtrafficer simply identified as Nkem Timothy, alias Auwalu Audu, in Sokoto State with 62 wraps of substance suspected to be cocaine weighing 1.550kg worth about N1bn According to NDLEA, the suspect, 36-year-old Nkem Timothy, alias Auwalu Audu, was arrested with 62 wraps of cocaine substance weighing 1.550kg, which has an estimated street value of about N1bn. The agency’s Director, Media and Advocacy, Mr. Femi Babafemi, mentioned that the suspect was arrested while trying to cross to Algeria through the Niger Republic. He quoted the acting state Commander of NDLEA in Sokoto, Bamidele Segun, as saying that the suspect was intercepted on a motorcycle around the Baggage area at Illela border while trying to cross to Niger Republic, with his final destination meant to be Algeria, where he resides. Daily Star Nigeria gathered that the illicit drug was neatly concealed inside Youghurt bottles. “He was found wit...

Da Dumi Dumi An Saka Ranar Mukabila Da Malam Abduljabbari Kano

Gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan watsa labaran jahar,  Muhammad Garba  da na ma'ikatar addin musulunci Muhammad Tahar ne suka sanar da kafar BBC Hausa lokacin da za a gudanar da mukabila da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara. Bangaren gwamnatin ya fitar da ranar lahadi 7 ga watan gobe na Maris a matsayin ranar da malaman jahar Kanon za su gwabza da Malamin. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kuma yi alkawarin samar da cikakken tsaro a lokacin gudanar da muhawarar ta ilmi. Wannan bukatar da malamin ya dade yana nema sai a wannan karo ya samu amincewar gwamnati a hukumance. TANTABARA za ta kawo muku yadda muhawarar za ta kasance.

Da Dumi Dumi Manyan Sojoji Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Saman Sojan Najeriya

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka sun tabbatar da faduwar wani jirgin saman soji kirar Boeng 350, daf da filin jiragen sama na Abuja, wanda wata majiya ke cewa na kan hanyarsa ne ta zuwa Mina ta jahar Naija. Ministan suhurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar da aukuwar lamarin, ta shafinsa na tweeter, in da ya ce an samu bayanin lalacewar dayan injimini jirgin tun farkon tashinsa. Wasu bayanan na daban sun ce ana fargabar akalla mutum 14 sun hallaka da suka hada masu mukamin janar biyu, da kaftin hudu, kofura biyu hadi da ma'aikatan jirgin hudu. An dai ga wuta na ci tare da tashin hayaki da ya game wurin, a daidai lokacin da jami'an kwana-kwana ke kokarin kashe wutar.

Alamu Na Nuna Gwamna Wike Zai Shiga APC

Bayanai da ke fitowa yanzu haka na bayyana alamun gwamnan jahar Rivers Nyesom Wike na daf da tsunduma jam'iyar APC mai mulki. An jiyo babban mai tsawatawa na majalisar wakilai ta tarayya Orji Uzo Kalu na bayar da tabbacin cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninsa da gwamna Wike. Kalu ya sanar da manema labaru a ranar alhamis cewa, bayan da gwamnan ya gayyace shi rangadin wasu ayukka da ke gudana a babban birnin jahar Fatakwal, ne suka tattauna kan wannan batun. Orji Kalu ya kuma ce sun shafe daren ranar suna shawarwari da gwamnan akan yadda zai shigo kana ya karfafa masa guiwa kan shiga jam'iyar APC, domin jawowa jahar ta Rivers alhairai masu yawa daga gwamnatin tarayya, in da kuma ya nuna yayi na'am da wannan shawara.