Skip to main content

Posts

Abdul'aziz Yari Zai Koma PDP

A yanzu daga kowane lokaci wata majiya mai tushe ta sanar da cewa jagoran jam'iyyar APC a jahar Zamfara, kuma tsohon gwamnan jahar, Abdul'aziz Yari zai bar jam'iyyar APC zuwa PDP. Tantabara News za ta kawo cikakken. Labarin nan gaba. KUNA IYA KARANTA:  http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/sabon-rikici-bangaren-abdulaziz-yari-ya.html

Shugaban Gwamnatin Jamus Frank-Walter Steinmeier Na Shan Suka

Jami'an Ukraine da na Poland sun soki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da cewa yana dasawa da  Rasha. Jakadan Ukraine a birnin Berlin ya kaurace wa wani bikin zaman lafiya da mawakan Rasha da Steinmeier ya shirya. Gidan rediyon DW ya ruwaito cewa, Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk da mataimakin firaministan Poland Jaroslaw Kaczynski  sun caccaki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier sakamakon alakar da aka lura yana da ita da kasar Rasha. Melnyk ya gaya wa jaridar Tagesspiegel cewa, "Steinmeier na da abin da ya ke boyewa dangane da wannan alaka tasa da Rasha". Ya kara da cewa, "mutanen da ke da alaka da Steinmeier kamar Jens Plötner, mai ba wa Wazirin Jamus, Olaf Scholz shawara kan manufofin kasashen waje, da Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus Andreas Michaelis hadi da karin wasu, na daga cikin wadanda ake zargin cewa ba za su rasa hannu ga wannan kusanci ba". Kaczynski ya kuma bayyana cewa manufofin ketare na Jamus na da tasg...

NDE Commences Sustainable Training and Loan Disbursement To 100 Youths in Sokoto

The National Directorate of Employment (NDE) has commenced Sustainable Agricultural Development Scheme (SADTS) and loand disbursement to 100 youths in Sokoto. Director-General of NDE, Malam Abubakar Fikpo, disclosed this on Tuesday in Sokoto during the orientation of agricultural loans disbursement held at Shamsuddeen Plaza. Fikpo represented by the Sokoto State NDE Coordinator Mrs Eunice J. Danmallam, said beneficiaries are entitled to N100,000 each at 9 per cent interest rate. He said the beneficiaries were captured under the Agricultural Enhancement Scheme (AES) and Community-Based Agricultural Empowerment Scheme (CBAES). He added they were also under Graduate Agricultural Empowerment Scheme (GAES) and Sustainable Agricultural Development and Empowerment Scheme (SADES). Fikpo said that six months moratorium was given after which  beneficiaries were expected to repay the loan in installments over a period of three years. Dan Mallam expressed gr...

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.

An Ga Watan Ramadan A Najeriya

An samu ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a yau kamar yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na Uku ya bayar da sanarwa. An ga watan a jahohin Sokoto da Kano da Katsina da Filato da Adamawa da sauran jahohi n Najeriya. Gobe asabar 2 ga watan Afirilu 2022 za ta zama 2 ga watan Ramadan 1443.

An Ga Watan Ramadan A Saudiyya

An ga jinjirin watan Ramadan a wurare da dama a kasar Saudiyya. Gobe asabar 2 ga Afrilu 2022 za ta zama 1 ga watan Ramadan 1443.

Zamu Yaki 'Yanta'adda Da Kanmu - El-Rufa'i

Cikin hushi gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta kasa kare al'umma daga harin 'yan bindiga to fa za su hada kai su kare jama'arsu, ko da kuwa ta kama su dauko sojojin haya daga ketare. Ya fadi hakan a wata hira da BBC ta yi da shi, in da ya ce dukan hare-haren da ake kai wa jama'a gamnatin tarayya na sane kuma sun san mazaunar 'yan ta'addan. Ya kara da cewa da jimawa shi kan sa ya sha ba shugaban kasa shawara akan matakan da ya kamata a dauka na yakar masu tayar da tarzoma da kisan jama'a a jahohin arewa maso gabas da arewa maso yamma amma sai a ka yi biris da shawarar da ya bayar.

Kwankwaso Ya Fice Daga PDP

Getty images Labarin da ke shigo muna yanzu haka sun tabbatar da tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fitar da sanarwar ficewa daga jam'iyyar ta PDP zuwa sabuwar jam'iyyar NNPP, jim kadan bayan da kotu ta bayar da umurnin dakatar da helkwatar jam'iyyar PDP ta kasa daga rusa membobin kwamitin zartaswar jam'iyyar reshen jahar Kano.

An Zabi Abdullahi Adamu Shugaban Jam'iyyar APC

Getty images Jam'iyyar APC ta cimma matsayar zabar tsohon gwamnan jahar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu, a matsayin sabon shugabanta. Kimanin 'yan takara shida ne suka janye daga neman mukamin, da suka hada da tsohon gwamnan jahar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura da tsohon gwamnan jahar Borno Ali Modou Sheriff da tsohon gwamnan jahar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar Mafara da sauran su. Tun da farko dai an bayyana Abdullahi Adamu a matsayin dan takarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke marawa baya.

Sabon Rikici: Bangaren Abdul'aziz Yari Ya Aike Ma Buhari Sako Mai Zafi

A wani abinda ake ganin bai rasa nasaba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nace akan samar da maslaha a zaben shugaban jam'iyyar APC na kasa maimakon gudanar da zabe, ya sa bangaren Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jahar Zamfara ya fito fili yana Allah wa dai da matakin shugaban kasa. Yanzu haka jam'iyyar APC na ci gaba da gudanar da babban taronta na kasa a Abuja. Ku latsa hoton da ke kasa don sauraren kalaman bangaren na masu goyon bayan Yari: