GAZA: Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya lalata wani dogon gini a birnin Gaza wanda ke dauke da ofisoshin kamfanin dillacin labarai na Associated Press da sauran kafafen yada labarai a yau Asabar, wannan farmakin sojin ya zo ne kwatsam ba tare da yin gargadi ga mazauna ginin ba, matakin da sojoji suka dauka na yin shiru a yayin fafatawarsu da kungiyar Hamas. Harin ta sama ya zo ne kasa da sa'a guda bayan da sojojin suka umarci mutane su fice daga ginin, wanda kuma ya hada da Al-Jazeera, da sauran ofisoshi da gidajen jama'a. Karfin harin ya ruguje daukacin ginin mai hawa 12, qanda ya haddasa turnukewar Æ™ura. Babu wani bayani akan dalilin da ya sa aka kai harin. Wannan sabon farmakin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani harin sama da Isra’ila ta kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke da yawan jama’a a garin na Gaza da ya kashe Falasdinawa akalla 10 'yan asalin dangi daya, wadanda galibinsu kananan yara ne, a wani hari mafi muni da aka kai a rikicin da k...