Skip to main content

Da Dumi Dumi Shugaba Idris Deby Ya Mutu

Shugaban kasar Chadi Idris Deby ya mutu a lokacin da ya jagoranci dakarun tsaron kasar a karshen mako, wadanda ke fafatawa da 'yan tawaye akan iyakar kasar da Libya da ke arewacin kasar.
Shugaba Deby wanda ake hasashen zai iya lashe babban zaben kasar da kashi 80 bayan ya nemi tsayawa takara a karo na shida.
Yanzu dai dakarun sojin kasar sun rosa rusa majalisar dokokin tare da bayar da sanarwar rike madafun iko na tsawon watanni 18 kafin gudanar da sabon zabe.
Idris Deby ya soma mulkin kasar Chadi a 1990 bayan ya yiwa gwamnatin tsohon shugaban kasar, Hissene Habry juyin mulki, in da kuma ya kwashe shekaru 30 akan karagar mulkin kasa ta Chadi.

Comments