Majalisar koli ta lamurran addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ta nemi da a hana musulmai masu shirin shiga itikaf don bautar Allah a wannan azumin Ramalana na bana, shiga kowane masallaci, sakamakon annobar korona na ci gaba da bazuwa a Najeriya.
Wannan matakin dai na zuwa ne daidai lokacin da 'yan siyasa da masu nadin sarautu ke ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin cin koso a Najeriya.
Ko a bara ma an dauki matakai masu alaka da hakan, da sunan kandagarkin annobar Covid-19. To sai dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, kasancewar da dama daga al'umma ne suka bijerewa umurnin.
Comments