Skip to main content

An Dakile Yunkurin Juyin Mulki A Nijar

Kwanaki biyu rak suka rage a rantsar da sabuwar gwamnati a Jamhuriyar Nijar wasu sojoji suka yi wani yunkurin juyin mulki a daren jiya talata.
Rahotanni da ke shigowa yanzu haka na cewa tun da misalin karfe 3:00 na daren jiya ne aka soma jiyo harbe-haben bindiga a fadar gwamnatin kasar.
Sai dai kamfanin dilancin labaru na AFP ya ruwaito cewa an dakile matakin.
A yau birnin Yamai ya zama cikin shirin ko-ta-kwana. Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani game da manufar wannan sabon yunkurin juyin mulkin da ma wadanda suka so kaddamar da shi.
Kasar Nijar dai ta dade tana fuskantar yawan juyin mulki tun daga lokacin sojoji ya zuwa yau. In da da dama daga shugabannin kasar da suka hada da Saleh Kumchey, Baare Mainasara har kawo Mammadou Tandja ake samun juyin mulkin sojoji.
Bayan kammala zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 28 ga watan Febrairun da ya gabata, wanda Bazoum Mohammed yayi nasara akan Mohammed Ousmane, ake sa ran a karon farko za a mika mulki daga wata gwamnatin farar hula zuwa wata.

Comments