Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2022

Rasha Na Shirin Kai Ma Amurka Da Kawayenta Hari

Reuters Rasha ta gargadi kasashen yammacin duniya da cewa za a dauki tsauraran matakin soji kan duk wani hari da za a kai a yankin na Rasha, tana mai zargin Amurka da manyan kawayenta da zagon kasa ga tsaron kasashen Turai ta hanyar tunzura Ukraine a fili ta kai wa Rasha hari. Yunkurin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya raba wasu miliyoyi da matsugunansu, ya kuma haifar da fargabar kazamin fada mafi muni tsakanin Rasha da Amurka, tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuba a shekara 1962. Watanni biyu tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, a cikin 'yan kwanakin nan Rasha ta ba da rahoton wani jerin hare-haren da sojojin Ukraine suka kai a yankunan Rasha da ke makwabtaka da Ukraine, kuma ta yi gargadin cewa irin wadannan hare-haren na da hadari sosai. Ukraine ba ta dauki alhakin kai tsaye ba, amma ta ce abubuwan da suka faru na mayar da martani ne, yayin da Rasha ta yi kakkausar suka ga kalaman da kungiya...

Ba Mu Yarda Da Sulhu Ba - Tambuwal

Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma yana daya daga cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya yi watsi da sakamakon taron da aka yi na amincewa da mutum daya da zai tsaya takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP a 2023. Gwamna Tambuwal ya yi watsi da hakan ne ta hannun daya daga cikin kungiyoyin yakin neman zabensa, Tambuwal Campaign Organisation (TCO). A cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun Daraktanta, Nicholas Msheliza a ranar Juma’a ta ce “Ofishin Kamfen din Tambuwal (TCO) ya ja kunnen wani labari cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi sun fito a matsayin ‘yan takarar da za zabi daya a matsayin maslaha daga cikin mu hudu, kuma wannan karya ce tsagwaronta sannan ba daidai ba ne “Gaskiyar lamarin ita ce kungiyar ta hadu a ranar Laraba 20 ga Afrilu, 2022, a masaukin Gwamnan Bauchi da ke Abuja, inda suka yi taron bita;  kuma, gaba É—aya sun yarda cewa tsarin yarjejeniya ba ya a...

NDE Disbursed 20,000 Naira as Loan to 228 Small Scale Business Owners in Sokoto

The National Directorate of Employment (NDE) has disbursed simple rate loan of =N=20,000 to 228 small business owners in Sokoto State.   Speaking on the occasion, held Thursday, at Shamsuddeen Plaza Sokoto, the State Coordinator, Mrs Eunice J. Danmallam said the NDE was established in 1987, and since then it has continued its creative work especially for young graduates and always keeps providing training and support to small business owners.  She added that under the current Director General of the NDE, Malam Abubakar Nuhu Fikpo, a number of measures have been put in place to help youths and small scale business owners by lending them low interest loans to repay within three months.   However, Danmallan said the agency has selected about 8026 Nigerians to benefit from the Programme, of which 228 are from Sokoto State.  The Sokoto State Coordinator urged the beneficiaries of the scheme to use the loans wisely, and then demanded that ...

Abdul'aziz Yari Zai Koma PDP

A yanzu daga kowane lokaci wata majiya mai tushe ta sanar da cewa jagoran jam'iyyar APC a jahar Zamfara, kuma tsohon gwamnan jahar, Abdul'aziz Yari zai bar jam'iyyar APC zuwa PDP. Tantabara News za ta kawo cikakken. Labarin nan gaba. KUNA IYA KARANTA:  http://tantabaranews.blogspot.com/2022/03/sabon-rikici-bangaren-abdulaziz-yari-ya.html

Shugaban Gwamnatin Jamus Frank-Walter Steinmeier Na Shan Suka

Jami'an Ukraine da na Poland sun soki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier da cewa yana dasawa da  Rasha. Jakadan Ukraine a birnin Berlin ya kaurace wa wani bikin zaman lafiya da mawakan Rasha da Steinmeier ya shirya. Gidan rediyon DW ya ruwaito cewa, Jakadan Ukraine a Jamus Andriy Melnyk da mataimakin firaministan Poland Jaroslaw Kaczynski  sun caccaki shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier sakamakon alakar da aka lura yana da ita da kasar Rasha. Melnyk ya gaya wa jaridar Tagesspiegel cewa, "Steinmeier na da abin da ya ke boyewa dangane da wannan alaka tasa da Rasha". Ya kara da cewa, "mutanen da ke da alaka da Steinmeier kamar Jens Plötner, mai ba wa Wazirin Jamus, Olaf Scholz shawara kan manufofin kasashen waje, da Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Wajen Jamus Andreas Michaelis hadi da karin wasu, na daga cikin wadanda ake zargin cewa ba za su rasa hannu ga wannan kusanci ba". Kaczynski ya kuma bayyana cewa manufofin ketare na Jamus na da tasg...

NDE Commences Sustainable Training and Loan Disbursement To 100 Youths in Sokoto

The National Directorate of Employment (NDE) has commenced Sustainable Agricultural Development Scheme (SADTS) and loand disbursement to 100 youths in Sokoto. Director-General of NDE, Malam Abubakar Fikpo, disclosed this on Tuesday in Sokoto during the orientation of agricultural loans disbursement held at Shamsuddeen Plaza. Fikpo represented by the Sokoto State NDE Coordinator Mrs Eunice J. Danmallam, said beneficiaries are entitled to N100,000 each at 9 per cent interest rate. He said the beneficiaries were captured under the Agricultural Enhancement Scheme (AES) and Community-Based Agricultural Empowerment Scheme (CBAES). He added they were also under Graduate Agricultural Empowerment Scheme (GAES) and Sustainable Agricultural Development and Empowerment Scheme (SADES). Fikpo said that six months moratorium was given after which  beneficiaries were expected to repay the loan in installments over a period of three years. Dan Mallam expressed gr...

Osinbajo Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

A jiya ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsaya takarar shugaban kasar Najeriya a 2023. Ya fadi hakan ne a lokacin wani kwarya-kwaryar buda baki da ya halarta tare da wasu gwamnonin jam'iyyar APC da suka hada da na jahar Kebi Abubakar Atiku Bagudo da na Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i da sauran su. A yau litinin dai ne Osinbajo zai sanar da wannan kudiri nasa a dokance, ta wani jawabi da za a yada ta bidiyo. Idan ana iya tunawa dai watanni biyu da suka gabata mataimakin shugaban Najeriyar ya ce ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan manufa tasa. Kafin bayyana wannan bukata, tuni dai wasu suka fito suka bayyana bukatar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC da suka hada da tsohon gwamnan jahar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello da Rochas Okorocha da kuma kwanan nan ministan suhuri kuma tsohon gwamnan jahar Ribas, Rotimi Amechi da sauran su.

An Ga Watan Ramadan A Najeriya

An samu ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a yau kamar yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na Uku ya bayar da sanarwa. An ga watan a jahohin Sokoto da Kano da Katsina da Filato da Adamawa da sauran jahohi n Najeriya. Gobe asabar 2 ga watan Afirilu 2022 za ta zama 2 ga watan Ramadan 1443.

An Ga Watan Ramadan A Saudiyya

An ga jinjirin watan Ramadan a wurare da dama a kasar Saudiyya. Gobe asabar 2 ga Afrilu 2022 za ta zama 1 ga watan Ramadan 1443.

Zamu Yaki 'Yanta'adda Da Kanmu - El-Rufa'i

Cikin hushi gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa idan gwamnatin tarayya ta kasa kare al'umma daga harin 'yan bindiga to fa za su hada kai su kare jama'arsu, ko da kuwa ta kama su dauko sojojin haya daga ketare. Ya fadi hakan a wata hira da BBC ta yi da shi, in da ya ce dukan hare-haren da ake kai wa jama'a gamnatin tarayya na sane kuma sun san mazaunar 'yan ta'addan. Ya kara da cewa da jimawa shi kan sa ya sha ba shugaban kasa shawara akan matakan da ya kamata a dauka na yakar masu tayar da tarzoma da kisan jama'a a jahohin arewa maso gabas da arewa maso yamma amma sai a ka yi biris da shawarar da ya bayar.