Skip to main content

Posts

'Yan Bindiga Sun Sako Hakimin Radda Alhaji kabir Umar

Rahotannin da ke shigowa yanzu haka, na cewa maharan da suka sace hakimin Radda, Alhaji Kabir Umar sun sako shi. Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da sakin nasa, sai dai ba ta yi cikakken bayanin yarjejeniyar da aka cimma kafin sakin sa ba. A ranar 22 ga wannan watan na Janairun makon jiya dai ne maharan suka sace ce shi daga Katsina zuwa dajin Zamfara. 'Yan bindigar sun sako shi a daren jiya bayan kwana hudu da sace shi. Rahotanni sun ce jami'an gwamnatun jahar Katsina da hadin guiwa da jami'an tsaro sun samu tattaunawa da maharan, abinda ya kai ga sakinsa, sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa kafin sakin na sa ba.

Sabuwar Kwayar Korona Ta Bulla A Najeriya

A halin yanzu da duniya ke tsakiyar fargaba da rashin sanin makoma, Hukumar Yaki Da Cuta Mai Yaduwa ta NCDC da ke Najeriya, ta fitar da sanarwar barkewar sabon nau'in cutar annobar korona da aka lakabawa suna B.1.1.7. Wannan sabuwar kwayar cutar dai ta fi ta farko saurin yaduwa da matukar hadari wajen kashe mutane, da aka tabbatar da ta kan yadu da kashi 70 cikin dari fiye da na farkon. A watan Disamban 2020 aka samu rahoton bullar sabuwar koronar a kasar Burtaniya da Afirka ta Kudu. Shugaban hukumar NCDC ta kasa Chikwe Ihekweazu ya sanar da hakan a jiya. Ya bayyana cewa hukumar za ta kara azama don yin kandagarkin bazuwar sabon nau'in korona na B.1.1.7 tsakanin jama'a. Wani kwararren likitan Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai suna Patrick Vallance, ya bayyana cewa, "daga marasa lafiya 'yan tsakanin shekaru 60 zuwa sama da suka harbu da tsohuwar kwayar cutar a kasar, 10 kan rasa rayukansu a cikin mutum 1000 kowace rana, amma a wannan karon, da wan...

An Rantsar Da Shugaba Joe Biden

An rantsar da shugaban Amurka na 46 Joe R. Biden tare da mataimakiyarsa Kamala Harris. Shugaba Biden ya nemi goyon bayan Amurkawa wajen samar da hadin kan kasa. "Ina neman hadin kan ku wajen ci gaba da ginin dimukuradiyarmu mai shekaru fiye da dari biyu ta ci gaba", in ji Biden. Ya kara da cewa, "Fatan da na sa gaba idan na shiga ofis, shine tabbatar da Amurka ta dore a yadda a ka santa, da inganta huldar dangantaka tsakanimu da waje, yaki da korona hadi da tabbatar da Amurka ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa". Shahararriyar mawakiyar nan, Lady Gaga ce ta rera taken kasar, haka ma mawakiya Jennifer Lopez ta nishandantar da mahalarta bukin. An dai gudanar da bukin cikin tsauraran matakan tsaro. Tun da safiyar yau tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bar fadar White House cikin wani jirgi mai saukar ungulu in da ya nufi jahar Florida. A can zai yi jawabin shirin kafa sabuwar jam'iyarsa da ya ce za ta samarwa Amurka makoma kasancewar manyan shugab...

Biden Ya Nemi Magoya Bayansa Su Tsaya A Gida Lokacin Rantsar Da Shi

A daidai lokacin da ake daf da rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden, an baza dubban jami'an tsaron soji domin murkushe duk wata zanga-zanga da ka iya barkewa. Tun a farkon makon da ya gabata ne dai Hukumar Leken Asiri ta Amurka ta FBI, ta yi gargadin cewa akwai yuwar samun tarzoma a ko'ina a kasar. Zababben shugaban dai ya shawarci jama'a da su yi zaman su a gida ba sai sun halarci bukin rantsarwar ba, ko baya ga matsalar annobar korona akwai yuwar dakarun sojin da aka baza na shirin maganin duk wanda ya nemi daukar dala ba gammo. Shugaba Donald Trump mai barin gado ya bayyana cewa zai bar babban birnin kasar Washington DC tun da sanyin safiyar gobe laraba, don kaucewa yin ido biyu da wanda zai gaje shi. A tarihin kasar dai wannan ne karon farko da za a yi bukin rantsarwa mafi tsaurin tsaro a Amurka, da kuma armashinsa ya ragu, muddin ta tabbata bai samu halarcin jama'a ba.

Akwai Yuwar Sake Rufe Makarantu A Nijeriya Saboda Korona

A irin yadda cutar korona ke ci gaba da kamari a duniya, mai yuwa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar na shirin bayar da shawara don sake kulle makarantu da zaran aka ga alkalumman masu kamuwa da ita na ci gaba da karuwa. An dai bude makarantun ne a ranar 18 ga wannan wata na Janairu, koda ya ke gwamnonin jahohin Kaduna da Edo ba su amince da bude makarantun ba. Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun gana da shuwagabannin kwamitin yaki da annobar korona don daukar mataki na gaba, da ake jin bai rasa alaka da sake rufe makarantun. Bayan bude makarantu a jiya, galibin al'ummar kasar sun yi suka akan matakin, da suka ce mai hadarin gaske ne saboda abu ne mai wuya hukumomin makarantu a Najeriya su iya cika ka'idojin da aka gindaya, kasancewar ajujuwa a makarantun makare suke da dalibai da zai yi wahala a bada tazara tsakani.

Wasu Daga Hotunan Gobarar Kasuwar Sokoto

DA DUMI DUMI Gobara Ta Kama A Babbar Kasuwar Sokoto

Tun da sanyin safiyar yau gobarar ta tashi a bangaren masu kayan robobi da ke Babbar Kasuwar Jahar Sokoto, abinda ya haddasa hasarar dukiyar da ba a kai ga gano adadinta ba a halin yanzu. Babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin hanyar da motocin kashe gobara za su bi, wanda wannan ya kara hayyaka matsalar gobarar da ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan kasuwar. Wannan ya sa masu dukiyar da ke ci gaba da konewa rashin sanin madogara, face diban kayansu da hannuwa ko don tsira da wani abu. Wasu da TANTABARA ta samu zantawa da su, sun bayyana cewa su kam sun tafka hasara, domin karfin wutar ba zai bar su fitar da wasu muhimamman abubuwa ba. To sai dai babu wani rahoton jikkata ko rasa rai kawo yanzu, wanda shi ne abinda ake fata.