Skip to main content

Posts

Gwamnatin Nijeriya Ta Karyata Kashe Masu Zanga-Zanga A Lekki

 Minjstan watsa kabaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya karyata rahoton kafar yada labaran CNN da ke cewa sojoji sun harbi da dama daga masu zanga-zangar Endsars a Lekki ta jahar Legas. Ministan ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce gwamnatin Najeriya za ta dauki mataki kan batun, da ya hada da rubutawa kafar ta CNN wasika akan ta karyata rahoton ko kuma duk abinda ya biyo baya kada su yi nadamarsa. A cikin wani bidiyo da kafar ta watsa an nuna sojoji na harbin masu zanga-zangar da harsashe na kwarai; har ma an ga wasun da aka harba kwance cikin jini. To sai dai tun a watan Oktoban da lamarin ya faru, hukumomin kare hakkin dan Adam da suka hada da Amnesty International suka fitar da rahotannin zargin harbin bindigar da ake alakantawa da jami'an soji.

LABARI DA DUMI DUMI

  Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar tarwatsa 'yan bindigar da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja. A kwanan nan 'yan bindigar masu garkuwa da mutane sun kashe akalla mutum 15 kan hanyar tare da jikkata da dama. Rundunar sojan ta bakin jami'in hulda da manema labarai Manjo Janar Enenche ta ce ta samu rahoton asiri ne dangane da 'yan ta'addan.

AN KUSA SHAWO KAN CUTAR COVID-19

 Rahotanni da ke fitowa yanzu haka sun bayyana cewa sabbin magungunnan rikagakafin cutar korona na nuna alamaun tasiri cikin gaggawa.  Kamfunnan Pfizer da BioNtech ne sahun gaba wajen samar da maganin, wanda an yi gwajinsa akan kimanin mutum 43,000 a kasashen duniya daban-daban tare da lura da cewa yana kashe cutar da kashi 94.5 kuma ba hi da illa. Masana kiyon lafiya a duniya dai sun bayar da shawarar ci gaba da amfani da rigakafin, sakamakon amanna da suka yi da shi. Ana sa ran samar da adadi mai yawa da zai wadaci al'ummar duniya nan da karshen shekara mai kamawa ta 2021, wanda ake muradin samun kimanin biliyan daya da doriya. Annobar korona da ta bulla tun a farkon 2020 ta kawowa duniya koma baya, wanda galibin kasashe masu karfin tattalin arziki suka gamu da cikas a bangaren tattalin arzikin, wanda ya shafi sassa da dama da suka hada da suhuri da yawo bude ido da ma cinikayya. Wannan yunkurin samar da rigakafin dai ana daukar sa a matsayin sabon kandagarki ga annibar Covi...