Kungiyar ma’aikatan jirgin kasa NUR da kungiyar manyan ma’aikatanta, SSA reshen layin dogo, sun umurci hukumar kula da layin dogo ta Najeriya NRC da ta tsunduma yajin aikin kwanaki uku a duk fadin kasar nan daga ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba, 2021, kan rashin walwala.
Shugabannin kungiyoyin biyu a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba, sun bayyana cewa wannan ci gaban ya biyo bayan wani taro da suka gudanar da hukumar NRC a ranar Laraba 10 ga watan Nuwamba.
A cikin takardar da aka gabatar wa shugabannin kungiyoyin na gundumomi da Sakatarorinsu na Legas, Ibadan, Inugu, Zariya, Minna, Bauchi, Kafanchan da dai sauransu, shugabannin kungiyoyin biyu na kasa sun umurce su da su kira taron ma’aikata a ranar Litinin mai zuwa domin sanar da ma'aikata game da yajin aikin da ke gabatowa.
Sanarwar ta ce: “Shugaban kungiyar ma’aikatan jirgin kasa (NUR) da manyan ma’aikatan NRC reshen NRC, a wani taron hadin gwiwa da suka gudanar a jahar Legas a ranar Laraba, 10 ga Nuwamba, 2021 inda sun tattauna akan lamarin da ya shafi jin dadin ma’aikatan kamfanin a matsayin a matsayin shimfidar tsunduma yajin aikin. Matsayar dabtaron ya cimma ta hada da:
“Dole ne DWC na NUR da SSA su dunkule, su ci gaba da aiki a matsayin kwamitin yajin aikin na gundumominsu kafin a fara yajin aikin na kwanaki 3 da kuma duk tsawon lokacin yajin aikin kuma za su tabbatar da cikakkar bin umurnin uwar kungiya.
“Ya kamata ma'aikatan su kasance cikin harabar hukumar kuma dole ne su kasance masu bin tsari da doka ta hanyar kare dukiyar jama'a ba tare da tayar da kowace iri tarzoma ba.
“Wannan yajin aikin da aka shirya shi ne kawai don aikewa da sakon gargadi ga gwamnatin tarayya domin biyan bukatu da inganta jin dadin rayuwar mai'aikata.
“Ya kamata shugabannin gundumomi na kungiyoyin su rika jiran umarni daga Legas lokaci zuwa lokaci kamar yadda jami’an kungiyoyin na kasa ke ganin ya dace.
"Kowace gundumar dole ne ta bi wannan sanarwar saboda duk wani aiki da ya sabawa wannan sanarwar za a duba shi da gaske kuma shugabannin kungiyoyin."
Bashir Ahmad Zubairu Dan Jarida ne a Najeriya
Comments