Hukumar samar da aikin yi ta kasa NDE, ta zabo matasa dubu daya daga Karamar Hukumar mulki ta Bodinga a Jahar Sokoto domin horas da su.
Shugabar Gudanarwar hukumar reshen jahar Sokoto Misis Eunice J. Danmallam ta bayyana cewa Hukumar NDE kamar kullum a shirye ta ke don yin hadin guiwa da gwamnatocin jahohi da kananan hukumomi da kamfunna da masana'antu kazalika da masu hannu da shuni domin tallafa al'umma a bangaren horas da su dabarun sana'o'i.
A cewa babbar jami'ar matasan da aka zabo za su koyi dabarun sana'o'i da suka hada da sana'ar walda da dunkin tela da gyaran famfo da kafintanci da hada man shafa da sauran su. Wanda wannan zai zama wani tsani da za su taka domin cimma madogara a rayuwarsu.
A nasa jawabi, wakilin Hukumar NDE na kasa a wurin taron Alhaji Mustapha Yakasai ya shawarci wadanda suka amfana da shiri da su dage wajen tabbatar da sun mayar da hankali wajen koyon tare da yin amfani da duka abinda suka koya domin amfanin kan su d sauran al'umma.
A nasu jawabai Sarkin Bodinga Alhaji Idris Abdul'uf da shugaban karamar Hukumar Mulki ta Bodinga wanda Alhaji Umar Magaji ya wakilta, sun nuna farin cikin su akan yadda hukumar ta NDE ta zabi Bodinga tare da bayyana cewa wannan gagarumin ci gaba ne da zai taimaka wajen rage radadin talauci a tsakanin al'umma.
Comments