Kalaman Dakta Ahmad Gumi da ya yi wa taken “Yaki bai taba zama mafita a ko ina” sun sabawa addini da hankali da tarihi da ma al'ada irin ta Bil Adama, domin kuwa addinin da tarihin su suka karyata su ba marubucin wannan shafin ba.
Yana magana ne game da hare-haren da sojojin Najeriya suka kai kwanan nan kan 'yan bindiga a Zamfara da sauran jihohin arewa maso yamma, wanda ya ce ba zai kawo karshen ta'addanci ba. Ya kuma ce tattaunawa da sulhu cikin lumana da shugabannin 'yan fashin kawai za su yi, kuma a cewar sa su ne kawai mafita.
Da farko dai, ba gaskiya ba ne cewa yaƙi bai taɓa warware wata matsala. Domin a cikin tarihin ɗan adam, babu abin da ke warware batutuwan da ke haifar da rikice-rikice a matsayin nasara face fagen fama.
Bari mu soma da addini, wanda shi ne jigo kafin kome ya biyo baya:
Al’ummar Musulmin farko a Madina sun sami nasarar tsira kuma a Æ™arshe sun yi nasara a kan maÆ™iyansu na Makka saboda yawan nasarar sojoji a Badar, Uhud, Khandaq da cin Makka a shekarar 629AD. Kafiran Makka sun fitini Manzon Allah ta hanyar azabtar da musulmi da kisansu da ma bautar da su. An umurce shi da yin hijira, wannan ba kome ba ne face matakin son zaman lafiya. Amma daga baya kafiran Makka su ka yi kokarin bin sa a can don yakarsa, da hakan ya haddasa Yakin Uhud, da musulmi suka samu nasara.
Da sun ci gaba da neman sulhu da ba a taka mu su birki ba.
Bari mu tsunduma tarihi din shi kuma, mu gani shin kalaman na Gumi gaskiya ne ko dai kawai jirwaye ne mai kama da wanka:
Tarihin duniya ya tabbatar da cewa sulhu da azzalumi ba zai taba kawo maslaha ba.
Misalai a nan da suka shafi kasashen turai na matsayin mizanin auna wannan magana. An samu nasara wajen dakatar da Napoleon Bonaparte ne kawai daga cin Turai ta hanyar samun nasarar sojoji a Rasha a shekarar 1812 da kuma a Waterloo a 1815.
Wanda akan tilas bayan an yi masa taron dangi ya mika wuya tare da sa hannu a yarjejeniyar ya fadi, da an tsaya neman sulhu shi ma da ba hakan ba ta faru ba.
Yaƙin Duniya na Biyu, yaƙi ne mafi tsanani a tarihin ɗan Adam, ya ƙare a cikin 1945 lokacin da Axis Powers suka karɓi buƙatun Allied Powers na "mika wuya ba tare da wani sharadi ba." Kazalika, shahararren sojan Amurkan nan Janar Douglas MacArthur ya fafata da kwamandojin Jafananawa a watan Agustan 1945 aka rinjaye shi kan tilas ya mika wuya.
Ba a kawo karshen yakin basasar Najeriya ta hanyar tattaunawa ba. Kwamandan runduna ta 3 Kanal Obasanjo ya amince da bukatar dakarun Biafra na sun yarda su ba da kai bayan an sha wuta saboda doguwar fafatawa.
Daga nan ya tafi da Babban Hafsan Hafsoshin Biyafara Phillip Effiong zuwa Legas don ganin Janar Gowon, inda ya karanta wani jawabi kuma ya ayyana, "Jamhuriyar Biafra ta daina wanzuwa tun daga lokacin."
Yaƙin basasar Amurka ya ƙare a cikin 1865 ba tare da tattaunawar zaman lafiya ba, bayan kwashe shekaru ana zubar da jini. Daga bisani dai a ka kawo karshensa lokacin da Babban Janar Robert E. Lee ya mika wuya ga Kwamandan Janar na Sojojin Tarayyar Ulysses Grant a Appomattox.
Hakanan, yakin basasar China na shekarun 1930 zuwa 40 ya ƙare lokacin da Mao Zedong da tsarin Kwaminisanci suka kwace iko da birnin Beijing a 1949 kuma suka ayyana Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin, yayin da Marshal Chiang Kai-shek da Kuomintang suka tsere zuwa Taiwan.
Dauki misali a baya, an warware yakin Jihadin Sokoto na 1804-08 a fagen daga. Shehu Usmanu Danfodio bai sanya hannu kan wata yarjejeniya da Sarkin Gobir ba saboda sojojin Jihadi sun kori Alkalawa kuma masarautar ta fadi. Haka ta kasance ga duk sauran masarautu a kasar Hausa.
Mummunan yakin basasar Kano na 1893-4, ya ƙare lokacin da Yusufawa suka fatattaki askarawan Sarki Tukur gaba ɗaya, suka bi shi zuwa Katsina suka kashe shi a can, wanda ba su nemi wani sulhu ba, da a ganin su neman tattaunawa ba zai kai su samun nasara ba.
A shekarar 1903 lokacin mulkin sarkin musulmi Attahiru Ahmadu, da sojojin Burtaniya suka kwace Sokoto, gwamnan turawan mulkin mallaka, Lord Lugard ya karanta wa Wazirin Sokoto cewa “Fulani a zamanin Danfodio sun ci kasar Hausa, su ne kuma ke mulki ba Burtaniya ba. Duk da ya ke idan an bi tarihi da kyau za a ga ba su yi sulhu da sarkin musulmi Attahiru ba, wanda kuma suka samu damar kashe shi a Burmi ta jahar Adamawa.
Wani misali mai sauki da zai nuna maka sulhu da 'yan tawaye ko 'yan ta'adda ba shi da riba shi ne yadda aka samu damar dakushe fitattun kungiyoyin 'yan tawaye a duniya.
Dubi yadda Tamil Tigers na Siri Lanka da 'yan tawayen FARC na Kolombiya da Sojojin masu turjiya na "Resistance Army" na Yuganda, RUF na Saliyo, Renamo na Mozambik,' yan tawayen Checheniya na Rasha, ETA ta Sifaniya, 'yan aware na Corsican na Faransa, Red Brigades na Italiya, Baeder-Meinhof da Red Army Japan duk an lura da yadda ta kare tsakaninsu da gwamnatocin da suke yi wa tawaye.
A halin yanzu, yakin basasar Siriya na da shekaru goma ana fafatawa ba tare da wata yarjejeniyar zaman lafiya ba saboda Shugaba Bashar al-Assad, tare da taimakon Rasha, Iran da Hizbullah, na ci gaba da ba shi taimakon domin ya kayar da 'yan tawayen da suka dauki makami a kansa.
Wani lamari ne daban idan 'yan tawaye suka sami nasarar korar gwamnati, kamar lokacin da' yan tawaye suka kashe Mu'ammar Gaddafi a Libya ko yadda 'yan tawayen Habasha suka kori Mengistu Haile Mariam a 199, ko yadda 'yan Somaliya suka kori Shugaba Siad Barre a 1991 ko kuma kwanan nan, kungiyar Taliban da ta kori sojojin Amurka daga Afghanistan; hada da juyin mulkin soji, kamar na baya -bayan nan a Gini.
Wanda wannan ya nuna idan har an ci gaba da neman tattaunawa da wani rikicin bai mutu ba har yanzu.
Nacewar Sheikh Gumi cewa dole ne gwamnati ta tattauna da 'yan bindigar arewa maso yamma ba daidai ba ne kuma ba zai yiwu ba. Da farko dai, 'yan fashin ba su da wata manufa ta siyasa ko maslaha da son cibgaban al'umma sai kisa da ruguza kasa.
Duk abin da suke da shi shine ƙaramin uzuri, cewa an mayar da su saniyar ware a Najeriya, don haka suka koma yin laifi. Sun yi kama da 'yan tawayen Janjaweed da suka tsoratar da gabashin Sudan shekaru 15 da suka gabata.
A shekarar 1992 lokacin da gwamnatin soja ta janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi rangwame da yawa kuma ta sanya hannu kan cikakkiyar yarjejeniya da Kungiyar Malaman Jami'a ta ASUU domin kawo karshen yajin aikin da take yi, sabon Ministan Ilimi kuma babban lauyan kundin tsarin mulki na lokacin Farfesa Ben Nwabueze ya yi watsi da yarjejeniyar cikin hanzari a watan Janairun 1993. Ya ce yarjejeniya ce “ingantacciya amma ba mai dorewa ba ”yarjejeniya ce da aka samar don gwamnati ta sasanta hakkinta na ikon raba albarkatu bisa zama da wani bangare na 'yan kasar don cimma manufa mai kyau, amma ba shi zai hanantaka birki ga mai neman wuce gona daniri ba".
Ko ta yaya, ba kamar Boko Haram ba, 'yan fashin ba su da wani shugabanci na tsakiya da gwamnati za ta iya tattaunawa da su.
Manufar su ita ce su kafa dauloli da dama ba bisa ƙa'ida ba a duk faɗin yankin inda za su iya kashewa, yi wa mata fyade da sace-sace yadda suke so.
Amurkawa suna bambanta tsakanin yaƙin "mai kyau" da "mara kyau". Sun ce Yaƙin Duniya na Biyu da mamaye Afghanistan shine yaƙe -yaƙe masu kyau yayin da Vietnam da Iraki munanan yaƙe-yaƙe.
Watau, idan an tilasta muku yaki kuma ba ku da wani zaÉ“i face kare kanku, kamar yadda 'yan fashi da Boko Haram ke yi, to wannan yaÆ™i ne mai kyau. Kai hari ga wasu mutane da sunan mamaye daula ko iÆ™irarin Æ™arya cewa suna da Makaman Kare Dangi mummunan yaÆ™i ne. Duka 'yan Boko Haram da' yan fashi sun kai hari kan Najeriya da al'ummarta. Fada da su da dukkan karfin da sojojin Najeriya da jami’an tsaro za su iya samu shi ne yakin da ya dace.
Amma duuk wani mataki sabanin wannan kuskure ne.
An lura sau tari fiye da shurin masaki, sheikh Ahmad Gumi na zuwa wurin jaje da tausayawa 'yan bindiga da sunan waye musu kai da yi mu su wa'azi amma ba a taba ganin sa yana zuwa jaje a wurin wadanda farmakin 'yan bindiga ke shafa ba.
Sai dai ba mu sani ba, ko wadannan matakan da ya ke ta dauka na a kare hakkin 'yan fashin shi ne abinda ya gani cikin addini?
Wannan amsa malamai ya dace su bayar da ita.
A sani na dai adadin yawan 'yan bindiga bai kai ko kashi daya cikin dari na yawan al'ummar Najeriya ba, kan haka ina dalilin ci gaba da kare su a duk miyagun ayukansu, amma a bar jaki ana dukan taiki?
Zubairu Ahmad Bashir
Dan jarida ne kuma mai sharhi akan al'amurran yau da kullum a Najeriya.
Comments