A wannan lokacin, yana da matukar wuya a gano labaran karya nan take ba tare da bincike mai zurfi ba.
Mutane na yada labarai marasa tushe a kokarin cimma wata mummunar manufa.
Misali na kwanan nan shine game da asalin Annobar Korona (Covid-19) da kuma tsarin sadarwa na intanet na 5G.
Wasu mutane kuma suna amfani da sunayen wasu shahararrun kamfanonin yada labarai wajen kaddamar da shafukansu na yanar gizon a Facebook. Za ku ga sunayen jaridu da kuka sani amma suna dauke da tambari daban-daban kuma wani lokacin ana rubuta sunayen ba bisa tsari ba.
Domin gano labaran karya a shafukan Facebook da tweeter, koyaushe a yi la'akari da abubuwan da ke ciki da tsarin harshen da aka yi amfani da shi wajen rubuta labaran.
Wani lokaci idan asusun na bogi ne zaka ga abubuwan da ke ciki ba a tsara su ba, babu rariyar likau kuma suna cike da kurakuran nahawu.
Lura, ku tabbata kun ga alamar tabbaci mai launin shuÉ—i da ke nuna cewa asusun na kwarai ne kamar dai na BBC.
Comments