Skip to main content

"Ba Zan Taba Sulhu Da 'Yan Ta'adda Ba" - In ji El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Tufa'i ya ce ba zai taba yin sulhu da 'yan bindigar da suka sace dalibai 39 a jihar Kaduna ba.
Ya ce, "ta yaya za ka dauki kudi ka ba dan ta'addan da zai yi amfani da shi ya sayi makamai wanda zai yi amfani da shi a kan ka".

A makon da ya gabata, ‘yan ta’adda sun sace dalibai 39 tare da neman kudin fansa har Naira miliyan 500 daga Gwamnatin Kaduna.
Gwamnan ya fada a watan jiya cewa ba zai taba yin sulhu da duk wani dan fashi da makami don neman kudin fansa ba.
Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na fuskantar yawan sace-sacen mutane, inda makonni biyu da suka gabata wasu mahara suka farma wani rukunin gidajen ma’aikatan Hukumar Filaye Jiragen Sama ta Kasa da ke Kaduna tare da yin awon gaba mutane 11 wanda kawo yanzu ba a san inda suke ba.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Iran seeks talks with us after threat of attack – Trump

U.S. President Donald Trump has said that Iranian authorities have contacted the United States to seek talks, following his threat to take military action over the killing of protesters in the country. Trump made the statement while speaking to journalists, saying that a meeting between the two sides has already been planned, but that the United States might take some action before the meeting takes place. Meanwhile, a human rights organization in Iran says it has confirmed the deaths of nearly 500 people since the outbreak of the protests. Likewise, some circulating video clips show a site outside Iran where bodies are being kept, with people going there to search for the remains of their relatives who have gone missing.