Skip to main content

Ba Kan Mu Aka Fara Ba - 'Yan Majalisar Zamfara

Gwamnatin jahar Zamfara ta sa kafa ta yi fatali da umurnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na hana shawagin jiragen sama a duk fadin jahar.
'Yan majalisar jahar sun yi kukan kura in da suka kada kuri'ar kin amincewa da wannan mataki da suka bayyana da ihu-bayan-hari.
Daya daga mahunkuntan da ya fito da kudirin har ya samu amincewa, Faruku Dosara yayi terere wa gwamnatin tarayya tare da raddi ga mai ba shugaba Buhari shawara kan lamurran tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, dangane da sakaci da ya zarge shi da yi kan lamurran da suka shafi tsaro da hukunta wadanda ake zargi da hannu ga sha'anin.
Kwanan nan dai ne aka yi garkuwa da daliban makarantar Sakandiren Kimiyya ta Jangebe su kimanin 300 da suka shafe kwanaki a hannun 'yan bindiga kafin sakin su, abinda masana ke zargin sai da aka biya kudin fansa kafin a cimma yarjejeniyar, lamarin da zai iya ci gaba da dagula matsalar tsaro a Najeriya.
Faruku Dosara ya ce, "ai ba jahar Zamfara kadai aka soma satar jama'a a Najeriya ba, akwai Dabchi da Kangara da Chibok ga kuma Kagara a jahar Naija, me zai sa Zamfara ta zama ta daban, to ba kan mu aka fara ba".
Ko baya ga satar mutane don neman kudin fansa hare-haren da 'yan bindigar ke kaiwa ya jawo hallakar daruruwan rayukan jama'a a jahar.
Wannan turka-turka da ta kunno kai ba a san in da za ta tsaya ba. Kwanan nan ma an jiyo gwamnan jahar Bello Mutawalle na cewa ba ya nesa ga fasa kwai don fallasa masu hannu a kashe-kashe da jerin hare-haren da ake kaiwa jahar ta Zamfara.

Comments