Skip to main content

Rikicin Jam'iyyar PDP A Kudu Maso Yamma

 

 Rikicin jam’iyar PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya na cikin kwale-kwale tun bayan da aka zabi gwamnan jahar Oyo Seyi Makinde jam’iyar PDP ke ganin ya na uwa da makarbiya a dukan lamurran da suka shafi jam’iyar, abinda suka ce na neman mayar da hannun agogo baya; kuma lamarin da wasu shuwagabannin jam’iyyar ke ganin shisshigi ne da kuma tare hanyar wasu.

A baya bayan nan gwamna Makinde ya dinga kai kawo a rikicin jam’iyar a jahar Ikiti da ya ce neman sulhu ne da shiga tsakani, amma hakan ya kai ga musayar yawu tsakaninsa da gwamnan jahar Peter Fayose na lokacin, wanda ke yiwa gwamnan jahar Oyon kallon mai goyon bayan Sanata Abiodun Olujinmi da ya tsaya takara tare da shi.

A halin yanzu an ji gwamnan na jahar Oyo na kurari da nuna goyon baya akan shari'ar da ake yi wa Fayose, in da Makinde ke ganin ya dace Hukumar Yaki da Zarmiyar Dukiyar Al’umma ta EFCC ta ci gaba tuhumar tsohon gwamnan jahar Ikitin.

Rahotanni sun ce an jiyo shi ya na cewa, duk yadda Fayose ya yi don kare kan sa, babu shakka sai an daure shi akan lafin da ya tafka. 

Da dama dai dag jiga-jigan jam’iyar PDP  yankin na Yarbawa na ganin kalaman a matsayin barazanar wargajewar jam'iyyar.

Comments

Wadanda aka fi karantawa

Gwamnatin Najeriya Ta Shirya Da ASUU

 An kai matsaya tsakanin Kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU in da gwamnatin tarayya ta amince da bukatunsu. A jiya jumu'a dai ne suka yi wani zama don ganin malaman sun janye yajin aikin da ya dauki watanni bakwai ana yi. A yanzu dai gwamntin Najeriya ta amince da cire malaman daga tsarin albashi na IPPIS wanda suka jima suna turjiya akai, kuma za ta biya malaman albashin duk watannin da su ke bi. Haka ma ministan kwadagon Najeriya Cris Ngige ya tabbatarwa manema labarai cewa, za a karawa malaman jami'ar alwus da zai kai naira biliyan 35 sabanin yadda yake a da na biliyan 30. Ngige ya kuma ce za a ci gaba da tattaunawa kan sabon tsarin albashi na UTAS muddin an kammala tsara shi. A nasu bangare kungiyar malaman jami'o'in sun yi maraba da wannan yunkuri, in da ake ganin matakin ga alama zai iya kawo karshen dogon yajin aikin da aka dade ana yi.